Kungiyar Daliban Jami’ar Bayero Aji Na 89 Ta Bada Gudummowa Ga Gidauniyar Marayu.

tsofin daliban jamiar Bayero

Kungiyar tsofin daliban jamiar Bayero dake kano aji na 89 sun bada gudunmawa ga gidauniyar tallafawa marayu ta Mallam Yushau Abubakar Tukur Dutse.

Dayake jawabi a gun bada gudunmawa a Masallacin Juma’a na Tukur Dutse Wakilin Kugiyar Muhammad Ibrahim somori yace sun bada gudunmawar ne domin tallafawa rayuwar marayu domin suma su sami rayuwa mai inganci .

Ya kuma yi Alkawarin zasu cigaba da tallafawa masu karamin karfin cikin Alumma domin fitarsu daga kuncin rayuwa.

Datake jawabin godiya Shugaba kungiyar marayun Hajiya Habiba Muhammad ta godewa wannan kungiyar ta kuma yi kira ga sauran kungiyoyin dasuyi koyi da wannan kungiya wajen kawo cigaba ga Alumma.

Shima Anasa jawabin Mallam Yushau Abubakar yayi nasiha kan tallafawa marayu a cikin addinin musulunci dakuma falalar da ake  samu.

Kusan marayu darine suka amfana da wannan tallafi Wanda ya hada da sabulun wanka da wanki.

Exit mobile version