Kungiyar Daraktocin Lafiya Ta Kasa Ta Karrama Ganduje

Daraktocin

Daga Ibrahim A Muhammad,

An karrama Gwamnan Jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje da matsayin wanda yafi bada gudummuwa a yaki da cutar sarkewar numfashi wato da a kafi Sani da Cobid 19.

Gwamnan wanda kungiyar daraktocin lafiya na kasa da aka kira ‘Nigerian Guild of Medical Directors’ ta karramawar a yayin taron da ta gudanar a Babban Birnin tarayya Abuja.

Kwamishinan ma’aikatar lafiya Dokta Aminu Ibrahim Tsanyawa daya wakilci Gwamna Ganduje ya ce Gwamnatin Jahar Kano karkashin jagorancin Dokta Abdullahi Umar Ganduje tana kashe makudan kudi a wajen yaki da cutar sarkewar numfashi saboda irin kokarin Gwamnan dan tabbatarda inganta lafiyar al’umma.

A lokacin mika Karramawar shima Babban sakatare na hukumar kula da Asibitoci masu zaman kansu Dokta Usman Tijjani Aliyu an karrama shi saboda aiki tukuru da yake wajen ganin tabbatar da inganta aikin lafiya.

Taron dai ya sami halartar jami’ai masu kula da harkokin lafiya a bangarori daban-daban a matakin kasa.

 

Exit mobile version