Wata kungiya mai suna Greater Kano Initiatibe (GREKIN) ta kuduri niyyar hada tattaki na musamman, don tuna alhinin da ya faru da wadanda su ka yi hatsarurruka a kan titina.
Bayanin hakan ya fito ne a sanarwar da kungiyar ta fitar a birnin Kano, jiya Laraba, ta na mai cewa, wannan tattaki zai faru ne a ranar Lahadi, 17 ga Nuwamba, 2019, da misalin karfe 9:00 na safe, inda wurin haduwa zai kasance Gidan Sarkin Kano na Nassarawa da ke kan titi Gidan Gwamna.
A wannan tattaki ne za su rarraba takardu da za su rika tunatar da masu amfani da titina kan illolin rashin bin dokar titi.
Wannan kungiya, wacce ta hada mutane daban-daban, amma masu ra’ayin cigaban jihar Kano, an kafa ta ne wasu watanni 18 da su ka wuce, kamar yadda bayanin ya wakana.
A cikin wannan lokutan ta ce, ta yi ayyuka da dama, wadanda su ka hada da taron masu ruwa da tsaki a kan harkar shaye-shaye da ya addabi jihar Kani.
“Akwai kuma agaji da ta bayar ga wasu daga cikin wadanda su ka tsinci kansu a cikin wannan hali ta hanyar wayar mu su da kai har da ma samar mu su da sana’a,” in ji sanarwar..
Wasu daga cikin abubuwan da wannan kungiya ta kuduri niyyar bada agaji a kai ya hada da bangaren ilimi, lafiya, noma da kuma mu’amulla ta yau da kullum.
“Yanzu haka GREKIN na da mabiya fiye da 300, kuma a kullum kara samun masu ra’ayin shiga ya ke yi,” a cewar sanarwar.
Ta cigaba da cewa, “a daidai wannan gabar, akwai wani taro na gangami da GREKIN ta ke shiryawa bayan wannan tattakin, wanda za a wayar wa jama’ar Kano yadda ayyukan majalisar jiha ta ke da ire-iren hukunce-hukuncensu. Don samun karin bayani a tuntubi wannan lambar 08034656535, 07039631848, 08135917001.”