Auwal Mu'azu" />

Kungiyar Hadejia Emirate Youth Ta Tallafa Wa Masu Kananan Sana’o’i

Godiya ta tabbata ga Allah madaukakin sarki me kowa me komai, Sarki gagara misali. a cikin ikon sa da kudirar sa ne muka samu damar kirkirar wannan kungiya mai albarka domin hada kan matasan kasar hadejia baki daya. Salati da yabo da girmamawa su kara tabbata ga shugaban mu Annabi Muhammad ,SA,W

farin jakada shugaban Annabawa da Manzanni, wanda Allah ya aiko shi dan ya zama shiriya ga mutane.

‘Yan uwana matasan kasar Hadejia, bani da abin da zan ce muku face godiya da fatan alkhairi. Duba da yanda kuka amsa kiran wannan kungiya don tabbatar da hadin kan matasan wannan masarauta tamu me tarin albarka. Bazan manta da irin cikakken hadin kai da goyon bayan ku ba, don ganin wannan tafiya tamu ta samu karbuwa a wannan kasa tamu, lungu da sako, Muna godiya da irin jajircewa da na mijin kokarin da kuke bamu, Mun gode.

An kirkiri wannan kungiya ne a Ranar 17th December, 2017. Wanda muka nemi shawarwari daga wajen manya daga bangarori da dama domin fara tafiyar, cikin ikon Allah duk wanda muka tuntuba, sai ya bamu goyon baya tare da bamu shawarwarin da zasu kaimu ga nasara. Daga nan bayan mun gama samun goyon baya sai muka fara tunanin yadda zamu tsara dokoki na kungiyar, wanda cikin ikon Allah muka kafa dandali na mutane biyar, wanda Barrister na kungiya ke jagoranta, bayan kammala kundin tsarin tafiyar da kungiyar da kuma buga shi a hukumance. Daga bisani kuma muka shiga fafutukar ganin mun yiwa kungiya rijista a hukumance, cikin ikon Allah bisa bin ka’idoji tare da gabatar da duk wasu takardu da kuma bayanai da ake bukata wajen yin rijista, muka dace aka yiwa kungiya rijista tare da bamu takardar shaida wato (certificate) na kungiya a ranar 10th Afrilu, 2018. Daga nan ne muka samu cikakkar shaidar fara gudanar da ayyukan kungiyar mu ba tare da fuskantar matsala ba, wanda kawo iyanzu muna da shugabanni da suke jagorantar kungiyar, da kuma mabiya masu tarin yawa, sannan sai iyayen kungiya.

Wannan Kungiyar an kirkirota ne domin hadin kan matasan mu tare da haskaka musu yadda alkiblar zamantakewar Al’ummar kasar hadejia zai kyautu ta kowanne bangare na rayuwa. Musamman idan akayi duba da yanda matasa ke da matukar muhimmaci a kowacce al’umma, wanda hakan yasa matasa ake kiransu da kashin bayan kowacce  al’umma. Wannan kungiya tamu bamu kirkirota domin cin zarafin kowa ba, ko kaskantar da wani mutum ko kuma nuna bangaranci ko wariyar yanki ba.

A’a sai don ganin mun hada kanmu waje guda mun zama tsintsiya madaurinki daya, domin kawo ci gaban yankin kasar mu mai dorewa, wanda ko bayan bama nan za’ayi alfahari damu a yankin Hadejia. Sannan wannan kungiya ba wai ta gwamnati bace, ko kuma ta wata Jam’iyya a siyasance ba, ko kuma ta wani mutum guda daya ko kuma ta wasu tsirarun mutane bace, A’a face kungiya ce mai zaman kanta ta al’umma musamman matasan yankin hadejia. Mutanan da suka kirkirota Matasa ne Hazikai, masu kishin yankin su wanda sun fito ne daga kananan hukumomin da suke karkashin masarautar Hadejia bisa hangen nesa da kuma gwagwarmaya na uban tafiya Chairman Muhammad Sani.

Kamar yanda sunan kungiyar mu ya nuna, kalmar hadin kai abune mai kyau tare da muhimmanci ga kowacce al’umma, sannan kuma hadin kai ibada ne kamar yadda rabuwa da lumana yake zamtowa sabawa Allah.

Idan har muka hada kan mu zamu so junan mu, kuma bukatarmu ma zata biya, idan kuwa aka ce babu hadin kai a tsakanin mu ko kuma muka rabu da juna to tabbas hassada, gaba, kyashi da kiyayya zata yi yawa a cikin mu, kuma hakika bukatarmu ma ba zata biya ba.

Hadejia emirate youth organization for unity and debelopment tasha fadi tashi wajen tabbatar da hadin kai da kuma kawar da kabilanci gami da bangaranci a tsakanin matasan yankin Hadejia

A ci gaba da kokarin da kungiyar hadin kan matasan yankin Hadejia take wajen kawo wa yankin Hadejia ci gaba,cikin ikon Allah tayi nasarar kawo kamfanin koyar da sana’o,in dogaro da kai ga al’ummar yankin Hadejia musamman matasanm maza da mata! Yayin da matasan suka yi nasarar samun horo daga  kwararrun ma’aikatan wannan kamfani.

Kimanin matasan sama da dubu   goma ne daga sassan Hadejia, gurin Malam Madori, Kirikasamma, Birniwa da kuma wasu kauyukan Auyo, Kaugama, Kafin hausa da Elleman ne suka samu horo daga wannan kamfani na (DREAM GATE WAY) domin koyon sana.o,in dogaro da kai

Bayan haka kungiyar tuni ta fara bada tallafi ga mata masu kananan sana’o’i rance daga naira dubu biyar zuwa sama domin su farfado da tattalin arzikinsu na gida, kuma cikin ikon Allah shiri yayi nisa sosai.

A fagen ilmi ma ba,a bar kungiyar ta Hadejia Emirate a baya ba, tuni sun fara shirin tallafawa yara dalibai, daga  JSS 1 zuwa SS 3 da shirin darussan taimakawa daliba (EDTRA LESSON)  wadda ta nemo kwararrun dalibai da suka kammala karatunsu a fannoni da daban-daban domin bada gudun mawar su ga kannensu ta yadda za,a samu bin yankin ilmin a yankin Hadejia da ma jigawa baki daya .

Duba da irin jajircewar wannan kungiya da take wajen kawo ci gaban ta ko wani fanni ne yasa al’ummar garin Karanka dake karamar hukumar Birniwa, suka jinjinawa wannan kungiya sanadiyyar wani kira da tayi wa gwamnati da a samar da ruwan sha a garin, kuma a kayi nasarar hakan.

Haka kuma suma mutanen garin Ayama, Kateje da kuma Hakudau sunyi wannan jinjina bisa hubbasawa da kungiyar tayi na kira ga gwamnati da a samar musu da hanyar shiga cikin garinsu, kuma anyi nasarar hakan cikin ikon Allah.

Kungiyar na taka muhimmiyar rawa wajen isar da sako ko korafin jama’a zuwa ga gwamnati musamman abin da ya shafi ci gaban al’umma baki daya .

Mai martaba sarkin Hadejia Alhaji adamu Abubakar maje da kuma sauran kusoshin yankin Hadejia sun nuna farin cikin su matuka, bisa irin wannan kokari da kungiyar ta (HEYOUD)  take wajen kawo ci gaba ga al,ummar yankin Hadejia.

Dattijai da kuma malamai harma da hakimai na yankunan hadejia emirate, sun gamsu sosai da wannan kungiya, inda suka yi kira ga matasa cewa su karbi tafiyar wannan kungiya yadda ya kamata domin hakan ne kadai zai iya basu damar kawo babban ci gaba mai amfani ga rayuwarsu da kuma al’ummarsu, sannan su kauracewa zaman banza, shaye shaye, bangar siyasa da kuma wasu munanan dabi’u marasa kyau.

Exit mobile version