Kungiyar Hamas Da Islamic Jihad Sun Amince Da Shirin Tsagaita Wuta Da Isra’ila

Isra’ila da kungiyar Hamas ta Falasdinawa da kuma Islamic Jihad sun bayyana amincewa da shirin tsagaita wutar da zai fara aiki daga karfe 2 na dare jiya a agogon yankin domin kawo karshen yakin da aka kwashe kwanaki 11 ana gwabzawa.

Sanarwar da ofishin Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya gabatar ta ce majalisar tsaron Isra’ila ta amince ba tare da hamayya ba shirin kasar Masar na tsagaita wutar ba tare da gindaya sharidodi ba.

Su ma kungiyoyin Hamas da Islamic Jihad sun tabbatar da shirin zagaita wutar.

Zuwa yanzu dai Falasdinawa 332 suka rasa rayukansu galibinsu fararen hula ciki har da mata da kananan yara, a luguden makaman roka fiye da 100 da Sojin Isra’ila suka harbawa yankin Gaza cikin kwanaki 11 da aka yi ana rikicin.

Hakazalika mutane fiye da dubu 1 da 600 suka jikkata yayin da ake fuskantar karancin abinci da magunguna a bangare guda kuma iyalai fiye da dubu 10 suka rasa matsugunansu sakamakon rushe-rushen da hare-haren na Isra’ila ya yi wa yankin.

Matakin tsagaita wutar ya biyo bayan kiraye-kirayen kasashen Duniya don daukar matakin Diflomasiyya da nufin shawo kan rikicin.

Exit mobile version