Kungiyar kare hakkin marubuta a Nijeriya ta (Human Rights Writers Association of Nigeria’ (HURIWA). ta nuna rashin jin dadinta wa shugaban ‘yan sandan Nijeriya Muhammad Adamu a bisa matakin ‘yan sanda na lakada dukan tsira, musgunawa da cafke mawallafin kafar Sahara Reporters Mista Omoyele Sowore a Abuja kashegarin sabuwar shekara.
A sanarwar da kungiyar ta fitar, ta shaida cewar kame Sowore wanda ke dauke da allon-tallar zanga-zangar lumana kamu ne wanda bai dace ba sam-sam, kuma ya saba wa dokokin kasa na baiwa kowa da damar zanga-zanga ta lumana.
kungiyar ta kara da cewa mai rajin gwagwarmaya domin jama’an ya fito ne domin shela kan ababen da suke tafiya ba daidai ba a kasar nan musamman kan matsalar tsaro da rashin mulki mai nagarta wanda kuma ke tafiyar da lamuran bisa lumana ba tare da wani tashin hankali ba.
HURIWA ta ce, yadda ‘yan sandan dauke da bindigogi suka musguna tare da kame Sowore da sauran masu zanga-zangar lumanar haramtacciyar kamu ce wanda hakan ya take ‘yancin walwalar dan adam tare da ‘yancin yin zanga-zangar lumana kamar yadda sashin doka 4 na kundin tsarin mulkin kasa ta 1999 ya baiwa ‘yan kasa damar yi.
kungiyar ta yi nuni da cewa, a maimakon ‘yan sandan su yi amfani da makaman hannunsu wajen yaki da ‘yan ta’adda da suka addabi shiyyar arewa maso gabas da arewa maso yamma sai suka bage da dira kan masu zanga-zangar kiran a dauki matakan gyara kan matsalolin tsaro.
“Dole ‘yan sanda su koyi yadda za su ke mutunta kwansitushin wanda ya baiwa ‘yan kasa damar kare musu kima da mutunci tare da hakkin ‘yan kasa. Abun da aka yi wa Sowore da ‘yan tawagarsa a Gudu da ke Abuja kwata-kwata babu inda suke barazana ga tsaron kasa ko Nijeriya,”
HURIWA ta bukaci shugaban kasar Nijeriya Muhammadu Buhari da ya bada umarnin gaggawa na gaggauta sake Sowore ba tare da wani sharadi ba shi da ‘yan tawagarsa.