Umar A Hunkuyi" />

Kungiyar IPOB Ta Bayar Da Sharadin Zaman Lafiya

A ranar Lahadi ne kungiyar ‘yan tawaye ta ‘yan asalin Biafra, IPOB, ta yi wani taron tattaunawa da shugabannin hadaddiyar kungiyar Igbo, ta, Ohanaeze Ndigbo da kuma kungiyar ta ‘yan kabilar Igbo wacce ke karkashin jagorancin Farfesa Ben Nwabueze, inda ‘yan kungiyar suka kafa wasu sharuddan zama lafiya da gwamnatin tarayya da kuma gwamnatocin Jihohin kudu maso gabas, da suka hada da, a janye sokewar da gwamnati ta yi wa kungiyar, da kuma yadda gwamnatin ta saka kungiyar a cikin jerin ‘yan ta’adda.

Hakanan kungiyar ta bukaci a kawo karshen duk wata tuhuman aikata laifi da ake yi wa ‘ya’yanta da aka kama a sassa daban-daban na kasar nan, a kuma yarda da ba su ‘yancin su kamar yadda tsarin mulkin Nijeriya ya bayyana ‘yancin duk wani dan kasa.

Taron wanda aka yi shi a gidan Farfesa Nwabueze, da ke Atani, ta karamar hukumar Ogbaru, a Jihar Anambra, sannan kuma kungiyar ta nemi da a biya ta diyyan duk ‘ya’yan na ta da aka kashe a lokacin kwamin da Sojoji suka yi da su mai suna, ‘Operation Python Dance,’ a can yankunan na kudu maso gabashin kasar nan, a kuma hukunta duk jami’an tsaron da suka aikata kisan na su.

Hakanan, jami’an tsaro su daina kowace irin musgunawa ga ‘ya’yan kungiyar da ke zaune a sassa daban-daban na kasar nan.

A lokacin taron, kungiyar ta IPOB, ta yi nu ni da cewa, a duk hukunce-hukuncen da aka zartarwa ‘ya’yan na ta, ba wanda aka same shi da aikata wani laifi ko kuma an daure shi ne sabili da samun sa da aikata wani laifi, don haka sai kungiyar ta ja daga a kan, tun da dai Ohanaeze, da kuma gwamnonin kudu maso gabashin kasar nan ne suka taru suka zartar da haramta kungiyar, to a yanzun ya zama tilas su sake wani taron su janye wannan haramcin.

Duk da cewa, tawagar kungiyar ta IPOB, wacce ta zo tun daga kasar Jamus, a karkashin jagorancin shugabanta, Aloy Ejimakor, sun dan fusata inda har suka fice daga zauren taron, kan abin da suka kira da, mummunan gabatarwar da aka yi ma su, da kuma rashin amsa bukatun na su kamar yanda suka bukata wanda shugabannin babbar kungiyar ta Ohanaeze su ka yi a wajen taron, amma dai sun yarda da su sake halartar wani taron wanda za a yi a ranar 8 ga watan Agusta, tare da dukkanin gwamnoni biyar na yankin na kudu maso gabashin kasar nan, domin sake tattauna bukatun na su sosai.

Da yake tattaunawa da manema labarai bayan taron na su, Farfesa Nwabueze, ya yi nu ni da cewa, batun  lakabin,’’Yan ta’adda,’ da aka yi wa kungiyar shi ne a kan gaba. Ya kuma nu na cewa, shugabannin al’umman na Igbo, da kuma shugabannin kungiyar ta Ohanaeze, duk sun yarda a yi duk mai yiwuwa domin ganin an janye haramtawan da aka yi wa kungiyar ta IPOB, ya kara da cewa, hakan ne zai samar da zaman lafiya a cikin kasar nan.

A cewar shi, neman zaman lafiyan ne ma ya sanya suke neman da a sake fasalin zamantakewa kasar nan, ya ce, matukar aka sake fasalin zaman kasar, to duk wani hankoron ballewa ya kare.

Farfesa Nwabueze, wanda ke tare da shugaban babbar kungiyar ta Ohanaeze, Cif Nnia Nwodo, da Bishof  Emeritus, Rt Rebd Madwell Anikwenwa, da sauran masu bauta na Yahudawa da sauran su, ya jaddada cewa, a irin wannan hali da siyasar kasar nan ke ciki da kuma lokaci, kabilar ta al’umman Igbo, ba ta da sha’awar fitar da shugaban kasa daga yankin na su.

Ya ce, amma dai taron na su ya tabbatar da bukatar jujjuya akalar shugabancin kasar nan a tsakanin sassan kasar nan shida, ta yadda kowane sashi zai tabbatar da ana damawa da shi.

 

 

Exit mobile version