Kungiyar Jam’iyyun Gama Kai Na Asibitin ATBUTH Ta Zabi Sabbin Shugabanni

Kungiyar jam’iyyun gama kai da adashen gata ta Asibitin koyarwa na jami’ar Abubakar Tafawa balewa da ke Bauchi ta zabi sabbin shugabanni da za su gudanar da ayyukan kungiyar da ke jagorancin ma’aikata kusan dari uku da suke zuba adashen gata na kusan naira dubu biyu a duk

karshen wata domin lura da matsalolin tattalin arziki na ma’aikatan asibitin da ke Bauchi.

Zaben wanada aka gudanar da shi ranar asabat da ta gabata an zabi Nuhu Malam Nuhu Manajan sashen lura da ido a matsayin shugaba Sai Malam Abubakar Sadik Ahmed a matsayin mataimakin shugaba da kuma Mohammed Yunusa Bekuta a matsayin Sakatare da kuma Abubakar Ladan a matsayin ma’aji. Har wa yau an zabi Ahmed Abdulhamid a matsayin mataimakin sakatare sai Zulai Baraya a matsayin sakatariyar kudi da kuma Nafiu Isiyaku a matsayin mai binciken kudi.

Kungiyar wacce aka kafa kusa shekaru shida da suka gabata ta himmatu wajen adana kudi daga albashin kowa na kusan naira dubu biyu a kowane wata saboda idan matsalar bukatar kudi ta taso kowane ma’aikaci yakan karba daga cikin ajiyarsa wani lokaci kuma sai a kara masa da rance inda ya zuwa wannan lokaci kungiyar ta bayar da kudi kusan naira milyan dari hudu don biyan bukatun yan kungiyar tun daga shugaban asibitin har zuwa kan lebura.

Sabodan shugaban Nuhu Malam Nuhu wanda ke cikin na gaba a wadanda suka kafa wannan kungiya cikin jawabinsa ya bayyana cewa za su ci gaba da aiki don hada kan ma’aikatan wannan asibiti da magance musu matsalolin kudi a duk lokacin da suka taso musu a karkashin wannan kungiya.

 

 

Exit mobile version