Connect with us

RAHOTANNI

Kungiyar Kabilar Atyap Ta Nemi Hadin Kan Fulani A Kan Zaman Lafiya

Published

on

Kungiyar cigaban Hadin kan Mazauna Atyap ta nemi Samarin Kungiyar Hadin Kan Fulani ta Bandiraku dake karkashin shugabancin Abbas J. Julde da Haruna Bello Laduga dasu hada hannu wajen nemo hanyar samun zaman lafiya a yankin.
A wata sanarwa da ya bayyana jiya a Kaduna, yayin maida martani game da tashin hankula da suka faru a garin na zangon kataf dake yammacin Kaduna, Shugaban Kungiyar ta kasa Professor Lucius J. Bamaiyi ne ya jawo hankulan Gwamnati da Jamian Tsaro akan barazanar Da Shugaban MACBAN, reshen Jihar Kaduna Malam Ibrahim Bayero Zango ya sanar.
Acewarsa, ” wannan sanarwar ta zama dole, saboda karerayin da kungiyar miyatti Allah ke yadawa a kamfanonuwan yada labarai game da tashin hankulan da suka faru agarin na zangon kataf da kewayen kauyukan Atyap tin ranar Laraba 10 Ga watan Yuni Shekarar 2020.
“Juma’ar data wuce, 5 Ga Yuni, 2020. Akwai jayayya data kware da Hausawa akan Gona dasuke gargadin Mazauna kuma ‘yan Asalin Atyap da subar noma a gonakinsu dake zagaye dagarin na zango”
“Shugaban mu Agwatyap da Jamian Tsaro sukai sulhu a tsakani.”
“A ranar Laraba 10 ga Yuni, 2020. Wani Malami Mr. Moses Yusuf Magaji, Dan shekara 32, ya tafi gonarshi dake gefen garin na zango, sai bai dawoba. Wasu matasa da Jami’an tsaro sukafuta nemanshi zuwa gonar dayatafi don Ciro amfanin gona. Ba a ganshiba a gonar sai dai anga wayar selularshi da kuma jini ta ko’ina acikin gonar.”
An cigaba da nemanshi a wannan ranar ta laraba har zuwa kashe gari da safiyar Alhamis 11 Ga Yuni, 2020. A lokacin ne aka samu gawarshi.
Atyap ya kara da cewa, lokacin ne matasan garin suka fara zanga-zangar lumana a yayin da Jami’an tsaro dake zango suka fara harbi kan mai uwa dawabi. Yanzu haka muna da matasa a asibitoci wadanda suka samu raunuka sanadiyyar harbin da Jami’an tsaro sukayi.
Ya kara da cewa, duk da hare-haren da aka kaimusu tsakanin shekarar 2017 zuwa 2020. Matsan Atyap basu taba daukar doka a hannunsu ba don ganin sun Wanzar da zaman lafiyar dake tsakaninsu da Hausa-fulani shekaru da dama.
ya kara da cewa, ” Kungiyar Miyatti Allah(MACBAN) suna canja gaskiyar magana don ganin sun kawo karshen zaman lafiyan dake a yankin ya koma tashin hankula da tarzoma.”
Yayi kira ga matasan Atyap dasu zama masu bin doka da oda da tabbatar da dawowan zaman lafiyan yankin.
Kuma Ina kara kira ga Hausa-Fulani mazauna yankin dasu hada hannu damu wajen kawo karshen tashin hankula, kuma babu daya daga cikin Atyap dake farin ciki da abunda ya faru.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: