Umar A Hunkuyi" />

Kungiyar Kamfen Din APC Ta Jinjinawa INEC

Jam’iyyar APC ta ce, ta gamsu da cewa, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, ta yi aiki mai kyau a wannan zaben da ya gabata.

Kwamitin kamfen na Jam’iyyar ta APC ya fadi hakan ne a ranar Litinin, jim kadan da Jam’iyyar PDP ta yi fatali da sakamakon zaben a kan abin da ta kira da an tafka magudi a cikin sa.

Kakakin kwamitin, Festus Keyamo, ya zargi Jam’iyyar PDP da kokarin ganin ta dawo kan mulkin kasar nan ko ta halin kaka.

“Ya zama tilas mu fitar da wannan sanarwan a kan hadarin yunkurin da babbar Jam’iyyar adawa ta PDP ke yi na ganin ta lalata zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 23 ga watan Fabrairu, 2019, ta hanyar sanar da wani sakamkon da ya sabawa dokar zabe.

Sanarwar ta ce, rahotanni daga dakin binciken yanayin zaben na Jam’iyyar APC sun nuna cewa, tabbas hukumar zabe ta INEC ta gudanar da aikinta kamar yanda dokar zabe ta tanada.

“Daga dukkanin rahotannin da muka samu daga dakin tattara bayanan zaben na Jam’iyyar APC a dukkanin sassan kasar nan, sun nuna cewa, hukumar zaben ta INEC ta yi kokarin gudanar da aikinta kamar yanda doka ta tanada, duk da irin kalubalen da ta fuskanta da kuma jinkirin da ta fuskanta a wasu wuraren. Tare da sama da mutanan da suka yi rajistan katin jefa kuri’a milyan 84, abin a yi godiya ne a kan yanda hukumar ta iya shiryawa tare da gudanar da zaben lami lafiya.

“Muna yin godiya ga dukkanin masu sa ido na ciki da wajen kasar nan a kan yanda suka sanya ido a kan zaben har ya gudana cikin tsanaki, gaskiya da adalci, kamar yanda suka shaida a cikin rahotannin da suka fitar a yau din nan.

A cewar Keyamo, sabanin ayyukan da suka sabawa doka da tsarin mulki wanda babbar Jam’iyyar adawa ta PDP da masu tausaya mata suke yi na umurtan a sanar da zaben da bai kammala ba, ta hanyar shelanta dan takaran su a matsayin wanda ya lashe zaben, inda suka cika kafafen yada labarai da sakamakon karya da suka yi sabani da gaskiyan lamari.

“Kar abokaninmu na sassan Duniya da ‘yan Nijeriya nagari su rudu. tun farkon fara gudanar da zaben, Jam’iyyar PDP da dan takaranta sun himmantu wajen kushe hukumar INEC. In za ku tuna, dan takaran su, Atiku, ya yi ta zarge-zarge marasa tushe ga hukumar ta INEC, da nufin sanyawa masu zabe shakku a kan hukumar ta INEC da kuma kokarin lalata shirin zaben gabadaya.

“Yin hakan, batunci ne ga tsarin mu na dimokuradiyya, kuma wulakanci ne ga milyoyin ‘yan Nijeriya da suka tudado suka sauke nauyin da ya hau kansu ta hanyar kada kuri’ar su. Abin takaici ne yanda PDP suka kudurci cewa, matukar ba su suka ci zaben ba, a shirye suke da su bi ko ta wace hanya don ganin sun komo kan mulkin kasar nan.

“Duk da irin matsayar ta rashin gaskiya da tsokana, muna da tabbacin sakamakon zaben da hukumar ta INEC ke fitarwa na gaskiya ne da adalci. Mun sami ci gaba a kan hanyar da muke gudanar da zabukan mu a ‘yan wadannan shekarun, kan haka muna neman PDP da kar ta yi kokarin mayar da mu baya da irin wannan wasan yaran da take yi. Ba da jimawa ba hukumar zabe za ta kammala sanar da sakamakon zaben da take yi. Mu kara hakuri, mu bar hukumar zaben ta gudanar da aikinta.”

Exit mobile version