Kungiyar Katar Charity Ta Tallafa wa masu karamin karfi 135 a Yobe

Katar

Daga Muhammad Maitela

 

Kungiyar Katar Charity ta tallafa wa maras karfi kimanin 135 da kayan sana’o’in dogaro da kai da suka hada da injinan markade, kekunan dinki, kekunan guragu da dabbobin kiwo tare da aza harsashen ginin cibiyar harkokin addinin musulunci a birnin Damaturu.

 

Maanyan jami’an kungiyar ne hadi da Gwamnan jihar, Alhaji Mai Mala Buni su ka halarci taron kaddamar da wadannan ayyukan tare da bayar da kayan tallafin a ranar Jummu’a, a babban birnin jihar dake Damaturu.

 

A jawabin Babban Daraktan kungiyar Katar Charity, Hamdi El-Saed Abdou ya bayyana cewa, “A 2019 ce mu ka halarci wannan muhalli don kaddamar da bude karamin masallaci wanda a wancan lokacin na dauki alkawarin gina cibiyar harkokin addinin musulunci wadda a yau gashi mun gabatar tare da na makaranta da shaguna, gidan marayu da dakin shan magani hadi da rijiyar burtsatse.”

 

A nashi bayanin, Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya bayyana jin dadin sa dangane da irinwwannan tallafin da kungiyar Katar Charity ta ke gudanarwa a fadin duniya, ya kara da cewa, “Wanda hakan wani hobbasa ne da tun da dadewa aka san Daular Bornu dashi wajen yada sakon addinin musulunci.”

 

“Har wala yau kuma, ko shakka babu da zarar an kammala ginin cibiyar zai taimaka wajen bai wa maluman mu tare da dalibai cikakkar damar ilmantuwa da gudanar da bincike mai zurfi dangane da addinin musulunci.”

 

“Kuma nayi imanin cewa za ta bayar da gagarumar gudumawa wajen dakile tsattsauran ra’ayi da yada gurbatattun akidun da suka yi ban-hannun riga da koyarwar musulunci. Za ta taimaka wajen gina ingantacciyar fahimta da koyarwar hakikanin sakon musulunci wanda Annabi Muhammadu (SAW) ya zo dashi.” In ji Gwamna Buni

Exit mobile version