Kungiyar Khadimiyya Initiatibe for Justice and Debelopment (KIJD) a jiya ta bada tallafin kekunan guragu guda dari biyu ga musakai a fadin kananan hukumomi 21 da ke akwai a jihar Kebbi.
Da ya ke jawabi a wurin taron bada tallafin kekunan a Birnin-Kebbi, shugaban kungiyar Khadimiyya na kasa Alhaji Malami Abdulkadir ya ce” kungiyar Khadimiyya Initiatibe for Justice and Debelopment wadda ministan Shari’a na kasa, Abubakar Chika Malami ya assasa tana son ta tabbatar da cewa dukkan musakai da ke da bukatar tallafin kekunan ko sanduna wanda ake amfani dasu wurin tafiya, wannan kungiyar ta basu tallafi a duk fadin jihar Kebbi da ma sauran wasu jahohin kasar nan, inji shugaban kungiyar Khadimiyya na kasa Alhaji Malami Abdulkadir yayin bada tallafin ga musakai a Birnin-Kebbi a jiya”.
Shugaban ya ci gaba da cewa” kungiyar Khadimiyya Initiatibe for Justice and Debelopment kungiya cewa mai zaman kanta, wadda ke kokarin ganin cewa ta bada tallafi ga masu karamin karfi da kuma gajiyayu da marasa galihu, haka kuma tana hadin kai da kungiyoyi masu irin manufar kungiyar Khadimiyya Initiatibe for Justice and Debelopment domin cinma manufufinta da kuma samun nasarar tallafawa al’ummar kasar nan, inji shi”. Hakazalika ya ce” wannan tallafi da aka bayar ga mutane fiye da dari biyu a jihar Kebbi taimakon ne daga wata Cibiya maisuna Beautiful Gate Handicapped Santa da ke a jihar filato, jos da suka taimaka wurin bada wannan tallafi, inji Alhaji Malami Abdulkadir”.
Yayin da ya ke bayyana yadda za a bada tallafin, keken zamani na musakai guda 165, keke mai kacha guda 30, kujerin musakai guda 10 Sai kuma sanduna na musakai guda 20 wanda fiye da musakai dari biyu zasu ci gajiyar wannan tallafi a fadin kananan hukumomi 21 na jihar ta Kebbi, inji shugaban kungiyar Khadimiyya Initiatibe for Justice and Debelopment na kasa, Alhaji Malami Abdulkadir.
Bugu da kari ya ce” sunayen musakan da suka ci gajiyar tallafin ya fito ne daga shuwagabannin kungiyar musakai ta jihar Kebbi wanda ya kunshi kananan hukumomi 21 a jihar, domin tabbatar da adalci ga musakan.
Haka kuma ya ce, “wadannan da suka ci gajiyar tallafin sun hada da masu kasuwarci da karatun da kuma koyon sana’o’in hannu na zamani,” in ji shi.
Daga karshe shugaban kungiyar Khadimiyya Initiatibe for Justice and Debelopment ya godewa shuwagabannin kungiyar musakai ta jihar Kebbi kan irin goyon baya da suke baiwa kungiyar ga gudanar da ayyukkanta na bada tallafi ga al’ummar.