Daga Muhammad Shafi’u Saleh, Yola
A kokarin gwamnatin tarayya na inganta fannin shari’a a kasar nan, kwamishinonin harkokin shari’a daga jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya Abuja na gudanar da wani taron yini biyu a Yola, domin lalubo hanyoyin magance matsalolin da ke haifar da tashin hankali a kasar.
Da yake jawabin bude taron, Kwamishinan shari’a na kasa kuma Ministan Shari’a Abubakar Malami (SAN) yace lokaci yayi da bangaren shari’a zai mayar da hankali ga irin matsaloli da ma barazanar tashe-tashen hankulan da kasar ke fuskanta.
Yace bisa matakan da gwamnatin tarayya ke dauka shi ne na hada kwamishinonin shari’a na kasar domin tattaunawa, a matsayinsu da suke da hakkin ganin doka tayi aikinta a kasar.
Malami ya ce, “Shi ne makasudin shirya wannan taron domin a zo da wani tunani tsayayye ta yadda za a fuskanci alkibla daya a ciyar da kasa gaba, kuma a samu kwanciyar hankali da lumana”
Ya ci gaba da cewa akwai dokokin da aka tsara, taron zai duba dokar a amince da ita a mataki na tarayya a kuma nemi fahimtar sauran jihohi ta fuskan kwamishinonin shari’a, domin su amince da yin dokar da kuma rungumarta a matsayin doka.
Ya jaddada cewa; “Taron zai duba dokar a amince da ita a matakin tarayya kuma zamu nemi fahimtar jihohi a kai saboda su amince a kafa dokar kuma su yi aiki da ita a matsayin doka”.
Haka shi ma da yake jawabi a taron, gwamnan Jihar Adamawa, Umaru Bindow Jibrilla, ya yi Allah wadai da irin hare-haren da kungiyoyin matasan IPOB ke kai wa al’umman arewa mazauna yankin kudu maso gabashin kasar, yace babban abin bakin ciki ne.
Gwamnan ya cigaba da cewa matsalar rikicin Boko Haram a yankin arewa maso gabas babban misali ne na koma-bayan da rikici ke haifar wa ga kasa, “Mu da mu ka ga rikicin Boko Haram ba mu goyon bayan kowanne irin tashin hankali, saboda da haka ina mai Allah wadai da rikicin kudu maso gabashin Nijeriya”.
Gwamna Bindow ya kuma bai wa al’umman jihar musamman Igbo mazauna Jihar Adamawa tabbacin tsaro da kare lafiyarsu a irin wannan yanayin da kasar ke ciki.