A shekaran jiya ne kungiyar kwadago ta bayar da sabon wa’adi na watan Disamba da ya zama lokacin karshe da gwamnatin Nijeriya za ta amince da karancin albashi na Naira 30,000..
Kungiyar ta yi gargadi cewa, ba za taba amince wa da rage ko sisin kwabo daga cikin Naira 30,000 da ta ayyana a matsayin ma fi karancin albashi, sannan kuma jinkirta amincewa ma da wannan bukata ba zai haifar da abu mai kyau ba.
Shugaban kungiyar ‘yan kasuwa Kwamared Bobboi Bala Kaigama da babban sakatare kungiyar manyan ma’aikata ta Nijeriya, Kwamared Bashir Lawal,su ne suka yi wannan gargadin a lokacin da suke yin mitin na a Chida Hotel, da ke Abuja ranar Talatar da ta gabata.
Suka yanzu haka ma’aikatan nijeriya sun sa idanu su ga cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da wannan doka ta karancin albashi.
A jawabin day a gabatar Kwamared Kaigama,ya bayyana cewa, abin da kungiyar kwadago ke sa rai shi ne a biya ma’aikata da wannan sabon tsarin acikin watan Disambar nan mai zuwa.
“Bisa wannan alkawarin da muka yi ne muke kira da babbar murya ga gwamnatin tarayya da ta tabbatar da wannan doka ta ma fi karancin albashi a matsayin Naira dubu 30,000,”.