Kungiyar Kwadago ta Kasa ta dakatar da yajin aiki da aka fara ranar Alhamis 26 ga watan Satumba daya gabata.
Shugaban kanugiyar Kwadagon, Ayuba Wabba ne ya sanar da haka a taron manema labarai da kungiyar ta kira ranar Lahadi a Abuja.
“Dakatar da yajin aikin ya fara ne nan take,” inji shi.
Wannan dakatar da yajin aikin na nufin kenan ma’aikata za su koma bakin aikisunranar talata kenan saboda tuni gwamnanin tarayya ta ayyana ranar Litinin 1 ga watan Oktoba a matsayin hutu don murnar ranar zagayowar ramar da kasar nan ta samu ‘yancin kai.
Ma’aikatan na neman a kara ne a kan karancin albashin da ake ba ma’aikata a kasar nan daga Naira 18,000 zuwa akalla naira 50,000.
Yawancin gwamnoni da ma’abota tsarin tarayya suna da ra’ayin cewa ya kamata a bar kowanne jihar ta tattauna tare da yanke abin da za su iya biyan ma’akatansu musamman ganin a kwai wasu jihonin da suka kasa biyan mafi karancin albashin da ake amfaniu da shi a ahalin yanzu na Naira 18,000.
A ranar Laraba ne shugaban kungiyar kwadagon, Ayyba Wabba ya ce, kofar kungiyar a bude yake don tattaunawa tare da tawagar gwamnatin tarayya a kan abin daya shafi yajin aikin.
“Bukatar mu shi ne a dawo da kwamitin dake tattaunawa a kan lamarin mafi karancin albashin don su ci gaba da tattaunawa domin karkare aikinsu.” inji Mista Wabba.
A nan ne Ministan Kwadago, Chris Ngige, ya tabbatar da cewa, kwamitin za su dawo bakin aikinsu don ci gaba da tattauanwa.
“Kafin zaman da za a yi ranar 4 ga watan Oktoba, za mu tabbatar da mun biya wa kungiyar dukkan bukatunsu,” inji Mista Ngige.