Abdullahi Sheme" />

Kungiyar Kwadago Ta Shirya Taro A Kan Sha’anin Tsaro A Jihar Katsina

A ranar Alhamis din da ta gabata ne hukumar kula da ayyukan kwadago da ingantuwar aiki ta jihar Katsina (Department of Labour & Productivity) tare da hadin gwiwar kungiyar kwadago ta kasa reshen jihar Katsina suka gudanar da taron fadakarwa akan sha’anin tsaro na kwana 2 a dakin taro na makarantar Bala Abdullahi College of Administration dake Funtuwa a jihar Katsina.
Tun farko a na shi jawabin mai ba Gwamnan jihar Katsina shawara a hukumar Kwamaret Tanimu Ibrahim Saulawa ya yabama Gwamnatin jihar Katsina domin da yardar maigirma Gwamna Alhaji Aminu Bello Masari aka gudanar da wannan taro na kwana 2 domin a kara lalubo hanyoyin magance tsaro a duk fadin jihar sannan Gwamna Aminu Bello Masari Gwamnatinsa a tsaye take domin kare rayukan Jama’a da dukiyoyin su a ko da yaushe kuma ya damu ganin yadda ake samun ta’addanci a wadansu kananan hukumomin jihar.
Kwamaret Tanimu Ibrahim ya ce, ma’aikatarsa tare da kungiyar kwadago ta jiha sun yi irin wannan taron akan sha’anin tsaro a yankin Katsina inda kananan hukumomi 11 suka halarta, ya ce, sun kira dukkan shuwagabannin Malaman makarantun firamare NUT da na kungiyar Direbobi na kananan hukumomi NURTW da Limamai da sauran Malaman Addini da kungiyar maaikatan lafiya da dai sauran kungiyoyi domin su bada gudummuwarsu wajen magance ta’addanci a jihar baki daya.
A lokacin gudanar taron anyi jawabai daban daban akan muhimmancin tsaro da kuma irin gudunmawar da kowanne mutum zai iya badawa.
Dakta Abdullahi wani malami a jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya ya gabatar da kasida mai taken “Rawar da Al’umma za su taka wajen magance ta‘addanci a kasar nan”, Dakta Abdullahi ya yi dogon jawabi wajen karanta kasidarsa a wajen taron ya cigaba da cewa, dole al’umma su san da wadanne irin mutane za su yi mu’amala ta yau da gobe kuma mutane su guji yawan yin surutu a ko ina kuma da zarar bako ya shigo kauyukan ku idan baku gane mashi ba a rika sanar ma da masu gari ko jami’an tsaro, kuma Gwamnatoci guda 3 su tashi tsaye wajen magance zaman banza da matasa ke yi kuma a samar masu da aiyukan yi tare da sana’oi, yace Gwamnatin tarayya ta samar ma dukkan jami’an tsaro kayan aiki irin na zamani sannan a kara yawan Jami’an tsaron kasar nan.
Dakta Abdullahi yace mutane su kula sosai wajen gano wadanda suke sharholiyarsu wajen facaka da kudade kuma an san mutanen basu da wata takamaiman sana’a ko aiki da zarar anga irin wadannan mutane a sanar da Jami’an tsaro don bincikar su.
Limaman Masallatan Juma’a na garin Funtuwa na kungiyar izala Sheikh Sa’idu Musa da na Darika Sheikh Abdurrahman Jibrin sunyi jawabai daban daban da kira ga Jama’a da su ji tsoron Allah kuma a cigaba da addu’oin samun zaman lafiya a yankin da jihar baki daya, a cikin manyan bakin da suka halarci taron akwai shugaban kungiyar ma’aikatan lafiya ta kasa reshen jihar Katsina kwamaret Mannir Skido da takwaranshi na kungiyar TUC Kwamaret Muntari Abdu Ruma da Shugaban Makarantar Bala Abdullahi College of Administration Funtua da Alhaji Shehu Lado Funtua

Exit mobile version