Kungiyar Kwadago Za Ta Shiga Yajin Aikin Kwana Uku A Kano

Kungiyar Kwadago ta kasa reshen Jihar Kano na shirin shiga yajin aikin gargadi na tsawon kwanaki  uku, Shugaban Kungiyar Kwadago na Jihar Kano Kwamared Kabiru Ado Minjibir ne ya bayyana haka alokacin taron manema labarai da kungiyar ta gudanar tare da hadin guiwar kungiyar samar da daidaito da al’amuran ma’aikata a Jihar Kano.

A cikin Jawabin na sa Kwamared Kabiru Ado Minjibir ya bukaci Gwamnatin Kano da ta dakatar da shirin da ta ke shirin farawa a watan Feburairun wannan shekara na dibar wani kaso daga cikin albashin ma’aikatan Jihar Kano a matsayin inshorar lafiya, har sai ta magance matsalolin albashi hadi da na kiwon lafiya.

Shugaban kungiyar na Jihar Kano yace akwai bukatar Gwamnati ta dakatar da shirinta na yin amfani da wasu kwararru  a tsarin biyan albashi tare da mika akalar shirin a hannun ma’aikata da suka cancanta, wanda ya yi daidai da tsarin  hukumar ma’aikata ta tarayya da kuma sauran jihohi makwabta kamar  su Jigawa da daidai sauransu.

Kwamared Kabiru Ado Minjibir yace ya lura cewa Gwamnatin Kano tana cire Naira dari uku da   saba’in da bakwai da kobo sittin (377.60) daga cikin albashin ma’aikata, da kuma a Naira dari da sittin da  takwas (168) daga bangaren ‘yan fansho ba tare gabatar da wani kwakkwaran dalili ba.

Ya ce dukkan wani kokari da muka yi a baya tun daga watan Nuwanba da disamba akan mu ga an gyara albashin ma’aikata a Jihar Kano bai samu ba, don haka daga karshe mun yanke shawarar cewar akwai tsari da gwamnatin Jihar Kano ta fito dashi na taimakekeniya kan harkar lafiya, wanda za’a fara cire kudi daga albashin ma’aikata daga wannan wata na Feburairu. Don haka mu ke kira ga gwamnati da ta dakatar da cire wadannan kudade na ma’aikata har sai, na farko an gyara albashin ma’aikata kowa ya san ma nawa ne albashin nasa kafin ya san nawa aka cirar masa, inji Kwamared Minjibir.

Har ila yau kuma Kwamare Minjibir ya bukaci Gwamnatin Kano data biya wadanda ta yiwa karin girma kudadensu dake aiki a matakin Jiha da kuma kananan hukumomi hadi da hukumar ilimin bai daya na Jihar Kano SUBEB. Ya ce lallai ne dukkan matsaloli wanda ya shafi rage albashi ko cirewa ma’aikaci wani abu, ko ma kwata-kwata mutun bai ga albashin na sa ba, ko a yanke masa wani abu ko da kuwa Naira dari biyu ce, lallai a dawowa da ma’aikata kudadensu domin hakkinsu ne.

Kwamared Minjibir ya ci gaba da cewa mun amince da cewar duka matsala ta ci gaban ma’aikata (Promotion) da kuma ci gaba na shekara shekara a kowa ne mataki ya zama wajibi a saka masu nan ba jimawa ba. Don haka zamu bi dukkan ka’idojin kungiyar kwadago ta bamu mu shiga yajin aikin jan kunne  na kwanaki uku inji, Kwamared Kabiru Minjibir.

 

Exit mobile version