Kungiyar Kwadago ta Kasa (NJC) reshen Jihar Kebbi ta shirya tsaf, domin tsunduma yajin aikin sai baba ta gani a duk fadin jihar ta Kebbi.
Bayanin hakan na kunshe ne a wata takardar da kungiyar ta Kwadago tare da hadin gwiwar sauran kungiyoyin hadaka na jihar a jiya da suka rubuta mai dauke da sa hannun sakataren kungiyar Kwadago na jihar ta Kebbi Kwamare SANI Muhammad Zuru da sakataren kungiyar TUC Kwamare Ibrahim Garba bayan kammala taron tattaunawa da suka gudanar a Sakatariyar ofishin kungiyar ta Kwadago da ke a Birnin-Kebbi, domin gudanar da tsare-tsaren yadda Yajin aikin zai kasance a duk fadin jihar.
Haka kuma takardar ta ci gaba da cewa” idan karfe 12 na Daren ranar Talata 6 ga watan Junairu na shekara ta 2021, gwamnatin jihar Kebbi bata biya bukatun da suka gabata na hakkokin ma’aikatan gwamnatin jihar ba, kafin wannan wa’adin da suka baiwa gwamnatin jihar na mako biyu da suka aikewa Gwamna jihar Kebbi tun a cikin watan Disamba na shekara ta 2020 data kare, idan ba a iya cika wa ba, lalle babu makawa zasu fantsama Yajin aikin sai baba ta gani, inji takardar da kungiyar Kwadago ta fito a jihar bayan kammala taronsu na tattaunawa kan yadda yajin aikin zai kasance”.
Daga nan shugabanin kungiyoyin na kira ga ma’aikatan jihar dasu bada goyon bayansu ga tsunduma fagen yajin aikin domin ganin cewa hakkokinsu sun fito daga hannun gwamnatin jihar ta Kebbi.