Sulaiman Ibrahim" />

Kungiyar Kwallon Kafa Ta Nijeriya Za Ta Buga Wasan Kawance Da Ivory Coast Da Tunisiya

Super Eagles za ta buga wasannin sada zumunci da Ivory Coast da Tunisiya a Austria a watan gobe.

A wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Tweeter a ranar Laraba, Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya (NFF) Amaju Pinnick ya ce Super Eagles za ta kara da Ivory Coast a ranar 9 ga watan Oktoba kuma bayan kwanaki za ta kara karawa da Tunisia a wani wasan.
Sakamakon jinkirtawa cutar coronavirus, Najeriya ta buga wasan karshe a watan Nuwamba na shekarar 2019, wasan neman cancantar shiga gasar cin kofin Afirka na 2021 da Lesotho a Maseru, wanda suka ci 4-2.

Haka kuma an shirya wa super Eagles buga wasanni biyu da Saliyo don neman tikitin shiga gasar cin Kofin Kasashen Afirka na 2021 a watan Nuwamba.

Ya kamata a buga wasannin a watan Maris ne, amma aka daga saboda cutar.

Najeriya ce kan gaba a rukunin da take tsallakewa zuwa gasar nahiyar, wanda yanzu za a buga a 2022 a Kamaru, da maki shida daga wasanni biyu.

Benin, Lesotho, da Saliyo su ne sauran kungiyoyin wannan rukuni tare da manyan kungiyoyi biyu da suka tsallake zuwa wasan karshe na gasar.

Exit mobile version