Daga Bello Hamza,
Kungiyar Lauyoyi ta kasa NBA ta mika sakon taya murnar bikin Kirsimeti ga ‘yan Nijeriya musamman lauyoyi.
Shugaban kungiyar, Mr Olumide Akpata, ya sanar da haka a takardar sanarwar da ya raba wa manema labarai a garin Legas ranar Juma’a.
“A yayin da muke taya juna murnar bikin Kiristimeti, ya kamata mu kuma rungumi juna a matsayin ‘yan uwan juna don ta haka ne za a tabbatar da samar da zaman lafiya da cigaban tattalin arzikn kasa.