Daga Khalid Idris Doya
kungiyar Likitocin Nijeriya wato ‘Nigerian Association of Resident Doctors’ (NARD) sun kimtsa domin shiga yajin aikin gama-gari a ranar Alhamis sakamakon rashin samun cikar bukatunsu da suke da su.
Wannan matakin na zuwa ne bayan da wa’adin kwanaki 60 da suka diba wa gwamnatin tarayya a ranar 25 ga watan Janairu ya kare dangane da matsalar biyan albashin da mambobin kungiyar ke bi a fadin kasar nan da kuma bukatar a sake nazarin alawus-alawus da ake biyansu tare da wasu bukatun da suke da su.
Sun yi korafi kan cewa, Alawus din Hazard na dubu biyar da ake biyan mambobin kungiyar ya yi matukar kasawa, kungiyar ta ce, tun lokacin da annobar Korona ta sanyo kai a shekarar 2020, cikin bakin ciki ta rasa mambobinta 17, wadanda suke cikin kauna da soyayyar iyalansu kafin mutuwarsu amma har zuwa yanzu ba su samu cin gajiyar tsarin Inshora ba.
A wata sanarwa da ta fitar a Abuja a karshen taronta na majalisar koli, shugaban kungiyar Dakta Uyilawa Okhuaihesuyi, ya ce bukatun nasu sun hada da biyan albashin da suke bi nan take da suka hada da na watan Maris kafin 31 ga Maris.
Ya ce: “NEC ta lura kan cewa tun bayan wa’adin da ta baiwa gwamnatin tarayya a watan Janairun 2021 a yayin ganawar majalisar kolinmu da ya gudana a Owerri zai kare ne a 31 ga watan Maris 2021 ba tare da cimma wata nasara ko guda daya ba.”
Ya ce, daga cikin bukatun sun har da batun biyan dukkan albashin da suke bi bashi ga mambobinmu na asibitocin gwamnatin tarayya da kuma na makarantun kiwon lafiya na jihohi.
Sun kuma nemi a sauya musu yawan alawus na afkuwar bala’i zuwa kashi 50 cikin 100 na albashin ma’aikata, sannan a biya alawus na aikin annobar Korona musamman a cibiyoyin lafiya na jihohi, wanda kungiyar ta ce tun lokacin da annobar ta auku mambobinta ke sadaukar da rayukansu wajen tunkarar annobar, “NEC ta iya fahimtar cewa duk da watanni uku sun shude da baiwa gwamnati wa’adi kan nemin sauyi wa tsarin biyan Alawus din rage radadin aukuwar bala’i ga ma’aikatan lafiya, har zuwa yanzu Hazard allowance dinmu na nan a naira dubu biyar a wata.”
“Bisa gazawar Rijistaran ‘Medical and Dental Council of Nigeria’ MDCN wajen iya tafiyar da bukatun da gwamnatin tarayya ta amince da su tun 2017, don haka muna neman a koreshi bisa gazawarsa kan shawo kan lamura,” inji kungiyar.