Muhammad Awwal Umar">

Kungiyar Magoya Bayan Hon. Bago Sun Yaba Da Tallafinsa Ga Matasa

Kungiyar magoya bayan dan Majalisar Wakilai ta Nijeriya mai wakiltar Mazabar Tarayya ta karamar Hukumar Chanchaga daga Jihar Neja, Hon. Muhammad Umar Bago, sun yaba wa dan majalisar bisa tallafa wa matasan jihar, musamman ’yan makaranta da ke karatu a manyan makarantun sassan kasar.

Shugaban kungiyar a karamar hukumar Rijau, Abdumajeed Mas’ud (Fashion B), ne ya yi yabon bayan wani zaman da su ka yi na yin kira ga dan majalisar, don ya fito takarar kujerar gwamnan Neja a zabe mai zuwa.
Matasan sun ce, “ba a samu wani dan siyasa a jihar da a inda duk ya hadu da kai a matsayin dan jihar da zai tsaya ya saurare ka kuma ya taimaka ma ka, kamar Hon. Umar Bago ba, domin mun fahimci ba karamar hukumar Chanchaga kawai ya ke wakilta ba; jihar ce ya ke wakilta a majalisar tarayya. Saboda haka a shirye mu ke goya ma sa baya a zaben gwamna mai zuwa, don mun san ya cancanta kuma ya san matsalolin da jihar nan ke ciki.
“Mu a yanzu ba karamar hukumar Rijau kawai ba, mun fantsama sauran sassan kananan hukumomi, don tallata shi ga jama’a, wanda mu na da yakinin zai karbu kuma jama’a za su goyi bayansa, domin kusan an ci moriyar wakilcinsa.”
Fashion B ya ce, “mu na kira da babban murya ga Hon. Bago da ya saurare mu kuma ya karbi kiranmu, don tsaya wa takarar kujerar nan, idan Mai Girma Gwamna Abubakar Sani Bello ya kammala wa’adinsa a shekarar 2023 mai zuwa.”
Matasan sun yaba wa jam’iyyar APC kan yadda ta ke tafiyar da siyasar cikin gida, wanda a na bai wa kowa damar tofa albarkacin bakinsa wajen tafiyar siyasa da kuma tafiyar da gwamnati, su na masu cewa, “mu kan a Rijau ba mu da wani bambanci, domin duk ra’ayinmu guda ne.”
Matasan sun nemi dan majalisar wakilan da ya hadu da ‘yan uwansa a mMajalisar Tarayya wajen ganin gwamnatin tarayya ta cika alkawarin da ta yi na cigaba da aikin hanyar Rijau zuwa Kontagora da kuma hanyar Mararrabar Yauri zuwa Rijau, don saukaka wa rayukan dubban jama’ar yankin, musamman ganin yadda hanyoyin su ka lalace su kan taba rayukan jama’a a lokacin ruwan sama, hakan ya janyo a na samun tsaiko da hasara mai yawa ganin yadda jama’a ke kaurace wa yankin saboda rashin hanya.
Matasan sun ce, “ba mu da wani wajen da yafi jihar nan, haka nan ba mu da wani abin alfahari da ya wuce Rijau, kyautatawa al’ummar mu zai kara taimakawa jam’iyyar APC samun galaba cikin sauki a lokacin zabuka masu zuwa nan gaba kadan.
“Mun jinjina wa gwamnatin jiha bisa damar da ta baiwa shugabannin mu a cikin tafiyar da gwamnati musamman ganin yadda shugaban karamar hukumarmu, Hon. Bello Bako, ya jajirce wajen ayyukan raya kasa. Don haka ba mu yi nadamar zaben jam’iyyar nan a dukkanin matakai na wakilci daga sama har kasa, za mu cigaba da marawa jam’iyyar nan muddin ta sahale wa Hon. Umar Bago tikitin takarar kujerar gwamna a zabe na gaba.”
Abdumajeed ya kara da cewar, “mu na kira da babban murya a kan kar Hon. Bago ya ja da baya wajen tallafa wa jama’a da yunkurinsa na ciyar da mulkin dimukuradiyya gaba.”
Matasan sun yaba wa dan majàlisar kan yadda ya fito karara ya bayyanwa duniya kasawar jam’iyyar APC kan matsalar tsaro da ta zamewa al’ummar yankin karfen kafa, wanda wajibi ne gwamnati a dauki sabbin matakai kan tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a, idan shugabanni suna daurewa suna fadawa gwamnati gaskiya lallai za a samar da shugabanci mai adalci a tafiyar siyasa.
Abdulmajeed ya jawo hankalin gwarzon nasa da kar ya yi sanyin guiwa wajen karfafa gwiwar matasa, musamman tallafin neman ilimi da sana’a, domin matasa su ne shugabannin gobe.

Exit mobile version