Daga Isa Abdullahi Gidan ‘Bakko,
A farkon wannan makon ne daukacin shugabannin kungiyar ma su makarantun Allo reshen jihar Kaduna suka ziyarci mai martaba Sarkin Zazzau Malam Ahmed Nuhu Bamalli a fadarsa da ke birnin Zariya,wannan ziyara da shugabannin suka kai wa mai martaba sarko ya sami rufin baicin shugabanin kungiyar na kananan hukumomin jihar Kaduna 23 da kuma fitattun mala,an addin musulunci da suke jihar Kaduna.
Tun farko a jawabinsa shugaban kungiyar na jihar Kaduna Gwani Malam SalisuAbubakar Fara Kwai, ya shaida wa mai martaba Sarkin Zazzau cewar, sun ziyarce shi ne domin yi ma sa ta’aziyyar rasuwar Iyan Zazzau Allhaji Muhammadu Bashari Aminu da Talban Zazzau, Alhaji Abdulkadir Pate Hakimin Igabi da dai sauran al’umma da dama da Allah ya karbi rayuwarsu a watannin da suka gabata.
Gwani Salisu ya kara da cewar, tun a lokacin rasuwar mai martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris, daukacin mambobi da shugabannin kungiyar na jihar Kaduna da na kananan hukumomin jihar Kaduna 23, sun ziyarci Fadar Zazzau inda suka yi ta’aziyyar marigayi sarkin Zazzau, a nan ne ya nana ta cewar, yadda mai martaba marigayi Sarkin Zzzau ya rungumi wannan kungiya da hannu biyu da kuma ba su tallafin day a kamata, wannan kungiya da shugabannin kungiyar ba za su taba manta wa da shi ba, na irin ci gaban da kungiyar ta samu, a dalilin kyawawan shawarwarin da ya ke ba su, a duk lokacin da suka kasance a gabansa.
suna wajen rungumar wannan kungiya a shekaru da dama da suka gabata.
A jawabinsa mai martaba Sarkin Zazzau Malam Ahmad Nuhu Bamalli, ya nuna matukar jin dadinsa da wannan ziyara da shugaban wannan kungiya suka kai ma sa domin yi ma sa ta’aziyyar wadanda aka bayyana sunansu da kuma addu’o’in da suke yi wa marigayi Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris.
Mai martaba Sarki ya kara da cewar, masarautar Zazzau za ta ci gaba da tafiya da wannan kungiya, tare dab a wannan kungiya duk tallafin da suke bukata.
Shi ma zantawarsa da wakilinmu sakataren kungiyar makarantun Allo na karamar hukumar Zariya Ustas Sani Bawa ya ce kungiyarsu a matakan jihad a kananan hukumomi da kuma gundumomi su na shirya taron karatun Alkur’ani mai girma, inda suke yin addu’o’I bayan kammala karatun Alkur’ani mai, domin karin samun zaman lafiya a karamar hukumar Zariya da masarautar Zazzau da jihar Kaduna da kuma kasa baki daya.
A dai zantawarsa da wakilimu Ustas Sani ya nunar da cewar, sun yanke shawarar yin karatun alkur’ani mai girma ne kuma domin kawo karshen kamfar tsaro da suka hada da garkuwa da mutane da kisar gilla da kuma sauran matsaloli da suke da alaka da matsalolin da suke addabar al’umma a ciki da wajen jihar Kaduna.
Da kuma Ustas Sani Bawa ya juya ga al’umma kafatan, sai ya yi kira garesu da su rungumi yin affu’o’I dare da rana, wanda in sun yi haka, wadannan matsaloli na tsaro da sauran matsaloli za su zama tarihi.
A lokacin wannan ziyara da wannan kungiya ta kai wa mai martaba Sarkin Zazzau, wasu daga cikin malaman da suka rufa wa shugabannin baya, sun yi addu’o’in tabbatan zaman lafiya a masarautar Zazzau da jihar Kaduna da kuma Nijeriya baki daya.