Daga Abubakar Abdullahi Lafia
Shugaban kungiyar Fulani makiyaya ta Miyyetti Allah a Jihar Nasarawa, Alhaji Muhammadu Husseini, ya bayyana shan alwashin kungiyar na hukunta duk wani makiyayi, da aka kama yana kiwon dabbobinsa a cikin gonakin jama’a. Shugaban ya bayyana hakan ne a wurin bikin rantsar da sababbin zababbun shugabanin kungiyar reshen karamar hukumar Kokona a fadar Abaga Toni da ke garin Garaku .
Alhaji Muhammadu Husseini wanda ya koka da halayen makiyaya masu shiga gonakin manoma suna kiwo, ya sanar da cewa kungiyar za ta rika daukar matakan ladabtarwa a kan irin wadannan makiyaya da ke shiga gonaki da gangan. Ya kara da cewar, “Mun kafa kwamiti kuma za mu kafa wani, wadannan kwamitoci za su bi hanyoyin da suka dace na hukunci ga duk makiyayin, da ya shiga gona da gangan ya da kuma bata amfanin gona”.