Connect with us

RIGAR 'YANCI

Kungiyar Makiyaya Za Ta Kafa ’Yan Sintiri A Jihar Kogi

Published

on

kungiyar Fulani makiyaya ta kasa (MACBAN) reshen jihar Kogi, tace ta shirya tsaf don kafa kungiyar yan sintiri domin yaki da matsalar tsaro data dabaibaye jihar.

Shugaban kungiyar a jihar, Alhaji Wakili Yusuf Damina ne ya bayyana hakan a bayan babban taron da kungiyar ta gudanar da mambobinta da ke jihar a karshen makon jiya a birnin Lokoja.

Kamar yadda shugaban yace,kungiyar ta MACBAN zata hada kai da jami’an tsaro na jihar domin kawo karshen rashin tsaro data yiwa jihar katutu.

Ya yi bayanin cewa muhimmin aikin kungiyar ita ce baiwa jami’an tsaro bayanan sirri game da harkokin masu satar jama’a da masu satar shanu da kuma yan bindiga wadanda ke yawan kai hare hare a yankuna dabam dabam na jihar.

Alhaji Damina ya yabawa gwamna Yahaya Bello a bisa tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a tsakanin manoma da fulani makiyaya a jihar.

Ya kuma ce fulani makiyaya da ke harkokinsu a jihar, a kowani lokaci zasu ci gaba da kasancewa masu biyayya da kuma bin doka da oda ganin cewa gwamnati ta basu tabbacin kare lafiya da kuma dukiyoyinsu.

Alhaji Damina har ila yau ya jinjinawa kwamishinan yan sanda na jihar Kogi, CP Ayuba Edeh a bisa kawo musu daukin gaggawa a duk lokacin da kungiyar ta MACBAN ta kai masa kuka, wanda hakan, a cewarsa ya taimaka matuka gaya wajen dakile rikici tsakanin manoma da fulani makiyaya a jihar.

Shugaban fulanin daga nan ya roki jama’ar jihar Kogi dasu sanya mambobin kungiyar ta MACBAN wajen yaki da matsalar tsaro da aikata laifufuka domin inganta zamantakewa da kuma ci gaban tattalin arzikin jihar.

Alhaji Damina wanda har ila yau ya bayyana godiyarsa ga gwamna Bello,ya kuma roke shi daya sanya fulani cikin mambobin majalisar zartaswansa kamar yadda yayi a zangon mulkinsa ta farko domin ganin sun bada gudunmwarsu wajen samun dawwamamen zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar ta Kogi.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: