Kungiyar malaman Kwalejin kimiyyya da fasaha (ASUP), ta ce za ta tsunduma yajin aiki na sati biyu a matsayin gargadi daga ranar 16 ga watan Mayu, 2022.
A sanarwar da ASUP ta fitar a ranar Laraba, ta ce, wannan matakin na zuwa ne bayan zaman gaggawa da Majalisar zartaswar kungiyar ta yi.
Sanarwar mai dauke da sa hannun Shugaban kungiyar ta kasa, Anderson Ezeibe, da aka mata take da ‘Halin da ake ciki tsakanin Gwamnatin tarayya da ASUP gami da matsayar da Majalisar zartaswar ASUP ta cimma’
Kungiyar ta ce ta dauki matakin janye wani yajin aikin da ta shiga ranar 6 ga watan Afrilun 2021 ne a ranar 10 ga watan June 2021 sakamakon rattaba hannun yarjejeniya tsakanin kungiyar da gwamnati da cewa su bai wa gwamnati damar wata uku domin ta samu sararin biya musu bukatunsu.
Kungiyar sai ta yi zargin cewa bayan wata tara da cimma yarjejeniya gami da tunatar da gwamnatin da suka yi, Gwamnatin ta kasa cika musu alkawuransu.
Kungiyar ta ce idan gwamnati ta kasa cika musu alkawuransu zuwa mako biyu da suka ware to za su tafi yajin aikin sai baba ta gani domin Neman gwamnati ta cika musu alkawuransu.