Daga Sulaiman Ibrahim
Kungiyar Ma’aikatan Kwalejin Fasaha (ASUP) za ta tsunduma yajin aiki a duk fadin kasar nan daga 6 ga Afrilu, 2021 kan zargin abun da ayyana da ‘’ al’adar sakaci da gwamnati keyi kan batutuwan da suka shafi bangaren ilimin kimiyya da fasaha. ’’
Shugaban kungiyar ASUP, Anderson U Ezeibe, ya shaidawa manema labarai a karshen taron da kungiyar ta gudanar a Kwalejin Hassan Usman Polytechnic, Katsina cewa akwai manyan kalubale shida da suka sanya kungiyar fadawa cikin wannan yajin aikin.
Ya ce gwamnati na ci gaba da gazawa wajen magance su tsawon shekaru.
Matsalolin, a cewarsa, sun hada da rashin aiwatar da yarjejeniyar ASUP / FG ta 2010, rashin biyan albashi da kuma biyan sabon mafi karancin albashi a wasu makarantun kimiyya da fasaha mallakar gwamnatin jihohi da sauransu.