Connect with us

LABARAI

Kungiyar Mamaye Za Ta Yi Taro Kan Aikin Ilmantarwa Da Kiwon Lafiya

Published

on

Kungiyar Mamaye da gamayyar kungiyoyin kiwon lafiya da na ‘yan jaridu wanda kungiyar Ebidence for Action ke jagorantar zama na musamman a kowane watanni uku a Jihar Bauchi, za ta yi zaman tattaunawa da masu ruwa da tsaki kan kiwon lafiya a ranar talata mai zuwa don wayar da kan jama’a a asibitocin yankunana karkara da biranen Jihar Bauchi. Har wa yau za a tattauna da kungiyoyin da suke taimakawa kan wannan aiki don samun bayanai kan nasarar da kungiyar ta cimma da kuma aikin da za a sa a gaba wajen inganta lafiyar mata da kananan yara a jihar Bauchi.
Shugaban kwamitin ilmantarwa kan inganta harkokin kiwon lafiyar mata da kananan yara na kungiyar mamaye Alhaji Ladan Isa Dalhatu, shine ya bayyana haka cikin ganawar sa da manema labarai, inda ya bayyana cewa aikin da aka dora masa yana da muhimmancin gaske wajen ganin an dukufa don shiga yankunanan karkara an ilmantar da mutane don su rika halartar asibiti a kan lokaci da kuma kai yara ana musu alluran rigakafi yadda ya dace.
Don haka ya bayyana cewa wannan kungiya ta himmatu wajen wayar da kai don haka ta kunshi ‘yan jarida da ma’aikatan asibiti da shugabannin kungiyoyi masu ruwa da tsaki kan harkokin kiwon lafiya don sune za su ci gaba da aiki tare kamar yadda aka saba don ganin an samu ingancin kiwon lafiyar mata masu juna da kananan yara fiye da halin da ake ciki a yanzu.
Don haka ya yaba wa jami’in kungiyar Mamaye Ebidence for Action Mista Laide Shokunbi, wanda ke kasancewa a gidan ma’aikatan kiwon lafiya Mahwun House da ke Bauchi a duk lokacin da za a yi irin wannan zama.
Haka kuma game da irin agajin da Mamaye ke yi kan kiwon lafiya a jihar Bauchi ya gode musu yadda ya kara da cewa suna basu karfin guiwa a kullum kan wannan aiki. Don haka ya ja hankalin kungiyar da cewa a shirye dukkan wadanda aka zaba wajen yi aiki don taimakawa kiwon lafiyar mata da kananan yara a Jihar Bauchi.
Ladan Dalhatu ya bayyana cewa kungiyar za ta fara gagarumin aikin jan hankalin gwamnatin Jihar Bauchi wajen ganin ta dauki ma’aikatan asibiti, saboda a ahalin yanzu yawancin asibitocin jihar Bauchi babu wadatattaun ma’aikata sai masu tallafawa da suka fito daga makarantun kiwon lafiya basu da aiki suke agazawa abin da ake kira bolontiya, don haka ya ce ya zamo wajibi a tashi tsaye don ganin gwamnati ta zauki ma’aikata don gudanar da ayyukan kiwon lafiyar jama’ar jihar Bauchi.
Musamman ganin wannan fanni yana bukatar wanda suka kware kuma an ki daukar aiki duk da haka sun amince suna taimakawa da tunanin idan an zo daukar aiki za a fara da irin wadannan mutane, kuma a shirye suke wajen ganin hakan ya tabbata a kowane lokaci a ka zo daukar sabbin ma’aikatan kiwon lafiya.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: