Sabo Ahmad" />

Kungiyar Manoma Dawa Ta Sha Alwashin Wadata Kasa Da Abinci – Muh’d Tahir

Manoman Masara

Shugaban kungiyar masu noman dawa na karamar hukumar kiru, ta jigar Kano, Ma’aru dahiru, ya bayyana cewa, ‘yan kungiyar ta su, sun yi alkawarin tallafawa gwamnatin tarayya da ta jihar Kano a kokarin da suke na wadata kasa da abinci da bunkasa masa’antunmu.
Shugaban ya bayyana hakan ne ga Editanmu, Sabo Ahnad Kafin-Maiyaki, jim kadan bayan kammala wani taron manoma dawa da suka yi a makarantar firamare ta Kwanar-dangoara, inda wasu daga cikin manoman, wadanda suka hada har da mata suka halarta, domin tattaunawa kan yadda za su bunkasa wannan sana’a ta su ta noma.
Tun da farko, Abba Muhammad dangora, wanda shi ke, babban malamin kona, mai kula da wannan yaki, a jawabinsa ya karfafawa manoman kan yadda za su bunkasa wannan sana’a ta su da kuma yadda za su ci moriyarta. Abba ya ci gaba da cewa, wannan lokaci da Allah ya kawo mu, lokaci ne da kullim darajar noma ke kara fitowa fili, saboda haka ne ma kullum manoman sai karuwa suke yi.
Don haka, sai ya shawarci dukkan al’umma su fito su rungumi wannan sana’a wadda za taimaka wajen wadata kasa da abinci da kuma bunkasa tattalin arziki.
Shi ma da yake tofa albarkacin bakinsa, sakataren wannan kungiya ta masu noman dawa, na wannan karamar hukuma ta kiru, Sa’adu Sani, ya ce, lokaci ya yi da al’ymma za su dawo cikin hayyacinsu, su dukufa kan noma, domin kuwa shi mafita daga dukkan wata wahala ta rayuwa.
Sannan sai ya yi kira da babbar murya ga manoma wajen samun hadin kai da bayar da goyon baya kan tafiya a kungiyance yadda za su amfana da shirin bayar da tallafin gwamnati da kuma samar da kasuwa ga anfanin gonar da suka noma yadda zai yi daraja.
A karshe, ma’ajin kungiyar, Hudu Sa’idu Gajale, ya yi kira da babbar murya ga manoman da ba su kafa kungiya ba, da su gaggauta yin haka domin cin moriyar sabbin tsare-tsare da gwamnati ta fito da su don tallafawa manoma.

Exit mobile version