Daga Mohammed Ali,
Shugaban hadaddiyar kungiyar manoman Nijeriya reshen Jihar Gombe, Mista Banyulla Halla, ya fito karara ya karyata rade-radin da ake yadawa cewa, kungiyar tana da wani bangare daban a jihar.
Kungiyar wanda a turance ake kiranta da ‘All Farmers Association of Nigeria (AFAN)’, ta reshen Jihar Gombe, ta samu kanta cikin rudani a ‘yan shekaru biyu ko uku baya, inda wasu membobi suke ikirarin cewa, kungiyar su ita ce sahihi wanda aka sani a hukumance a jihar yayin da wasu kuma suke cewa, kungiyar su ce sahihi.
Sai dai da yake mayar da martani a kan wannan rudanin ya da ya ki ci yaki cinyewa, Mista Banyulla ya sanar wa da manema labarai a ranar Talata na wannan mako a ofishin kungiyar dake a tsakiyar cikin garin Gombe cewa, shi bai yarda akwai wani bangare na AFAN, yana mai cewa, shi tunda aka zabe shi shugaban kungiyar a 2015, har zuwa yanzu, shi ne yake shugabancin ta.
A cewar shi: “Babu wani bangaren a AFAN a jihar Gombe, masu irin wannan furucin, rudani kawai suke ta yi domin cimma burinsu na raba kawunan manoman mu. Kungiyar AFAN daya ce a Gombe, kuma nine shugaban ta tun 2015 har zuwa yau”.
Mista Banyulla sai ya yi kira ga masu kururwar cewa akwai bangaranci a kungiyar, da su mayar da wukar, su zo a tafi tare domin ciyar da manoman Jihar Gombe gaba saboda a cewarsa, “Irin wannan fitina, rudanii kawai zai haddasa a tsakanin manoman mu wadanda suka dogara da Allah da kuma wakilcin mu. Kofa ta a bude take a ko da yaushe”.
Ya ce a halin da ake ciki yanzu, dubban manoma a kananan Hukumomin Yamaltu-Deba, da Funakaye da Dukku da Nafada da Balanga da kuma Kwami, sun ci gajiyar kungiyar da tallafin taki domin noman rani, kuma nan da mako guda duk sauran kananan hukumomin jihar za su samu nasu kason na takin wanda ya ce, shirin tallafin hadaka ne da bankin kananan masana’antu ta Jihar Gombe (wato Gombe Micro Finance Bank).