Alhussain Suleiman" />

Kungiyar Masu Sayar Da Magagungunnan Daddobi Sun Ziyarci Sarkin Kano

Magagungunnan Daddobi

Kamar yadda kungiyoyi da masoya tare da yan’uwa da abokan arzuka ke ci gaba da ziyara tare da mubaya’a ga Sarkin Kano, Alhai Aminu Ado Bayero.

Suma kungiyar masu sayar da magungunan Dabbobi ta jihar Kano, ta kai irin wannan ziyara tare da nuna mubaya’a ga Sarkin na Kano, kamar yadda mataimakin shugaban kungiyar na ihar Malam Sabi’u Rabi’u Chedi ya shaidawa manema labarai haka in kadan da kammala ziyarar da ya samu halartar daukacin yankunyar.

Malam Sabi’u Rabi’u Chedi, makasudin kai ziyarar shi ne domin su ta ya shi murna da farin ciki na zaman towar shi sarki Kano, har ila yau su kuma gabatar ma shi da manufofin kungiyar kungiyar da kuma samata albarka, matsahin dankasuwar ya ce wannan ziyarar ita ce ta farko da suka kaiwa sarkin .

Da yake gabatar da jawabin shi ga kungiyar inji mataimakin shugaban kungiyarm ya ce sarkin ya nuna gamsuwar shi tare da farin cikin  da ziyarar da aka kawo ma shi ya kuma tabbatar masu da cewa zai ba su hasin kai da goyon baya tare das u shawarwari masu kyau domin ciyar da kungiyar gaba da yardar Allah.

Da yake tsokaci game da kungiyar ta su mataimakin shugaban kungiyar ya nuna matukar farin cikin shi game da yadda kasuwancin sayar da magungunan dabbobin ke kara samun cigaba idan ka kwatanta da shekarun da wasu kabilune kawai suke gudanar da sana’ar a fadin jihar.Amma yanzu kusan duk inda ka samu mai wannan sana’ar bahause ne musamman danjihar Kano.

Sai Chedi ya shwarci yankungiyar da su kara baiwa shugabannin kungiyar hadin kai da goyon baya domin acimma nasarorin da ake bukata, har ila yau su tabbatar sun tsare gaskiya da amana acikin gudanar da harkokin sun a kasuwanci da sauran al’umma masu cinikin kayan su .

Daga karshe Alhai Sabi’u Rabi’u Chedi, ya yi addu’ar Allah ya kara baiwa jihar Kano da kasa baki daya zaman lafiya da bkaruwar arziki

Exit mobile version