Khalid Idris Doya" />

Kungiyar Mata ‘Yan Jarida Ta Raba Tallafin Kayan Jinya A Bauchi

Daga Khalid Idris Doya, Bauchi

 

Kungiyar mata ‘yan jarida ta kasa (NAWOJ), reshen jihar Bauchi sun raba tallafin kayyakin jinya na dubban naira wa iyaye mata a jihar ta Bauchi, hakan na cikin bikin da suka gudanar na makon rikafi ta Nahiyar Afirka wanda ya gudana a Bauchi.

Tallafin kayyakin jinyar wanda suka rarraba wa iyaye mata a asibitin amsar haihuwa da ke Bayan Fada a cikin Bauchi domin karfafa musu guiwa kan lafiyarsu da na ‘ya’yansu.

Da take jawabinta a wajen rabon kayyakin da kungiyar mata ‘yan jaridan suka raba, Sakatariar NAWOJ reshen jihar Bauchi, Aisha Bamai ta bayyana cewar sun yi hakan ne domin su karfafa iyaye mata wajen tabbatar da suna samar wa ‘ya’yayensu allurar rigakafi domin dacewa da alfanunsa a garesu.

Mrs Aisha ta bukaci iyaye a dukkanin matakai da suke yin duk mai iyuwa wajen tabbatar da cewar yaransu suna amsar nagartaccen rigakafi domin kariyan kai daga dukkanin wata cutar da ta ke kisan yara ko wanda ta jibinci hakan.

Sakariyar ta NAWAJ wacce ta wakilci shugaban kungiyar ta jihar Bauchi Bulak Afsa ta ci gaba da kiran iyaye da su ke tabbatar da tsaftar mahalansu da kuma wanke hannayensu domin kariyan kai daga kamuwa da cutattukar da ake iya kamuwa da su ta fuskacin rashin tsafta da sauransu.

A nata jawabin kuma, Sakatariyar kungiyar mata ‘yan jarida a shiyyar Arewa Maso Gabas, Hajiya Halima Ibrahim ta bukaci iyaye ne da su yi fatali da dukkanin wani rade-radin da ake yi musu akan rigafi, tana mai cewa rigakafi na da matukar fa’ida ga yara ‘yan kasa da shekaru biyar, wajen samar musu da nagartaccen lafiya da kuma kafiyan kai daga kamuwa da cututtuka.

Jami’in da ke kula da sha’anin rigakafi a karamar hukumar Bauchi, ya jinjina da irin wannan na-mijin kokarin da kungiyar mata ‘yan jarida suka yi da kuma wanda suke yi wajen fadakar da jama’an kan sha’anin kula da lafiya, yana mai kiran kungiyoyin mata daban-daban da su yi koyi da kungiyar ta NAWOJ domin tallafa wa sha’anin lafiya a jihar.

A wani taron manema labaru da suka yi, Daraktan kawar da cututtuka da rigakafi na jihar Bauchi Mrs Lois Daniel ya bayyana cewar makon ta rikafi na Afirka an samar da shi ne domin wayar da kai dangane da muhimmancin rigakafi da kuma kuma alfanunsa ga rayuwar jama’a musamman ga yara ‘yan kasa da shekaru biyar.

A nasa jawabin kuma, Jami’in hukumar lafiya ta duniya a jihar Bauchi (WHO), Dr Adamu Ningi ya bayyana cewar muhimmancin rigafi na da matukar yawa, yana mai kira ga masu ruwa da tsakiya, iyaye, sarakuna, malamai da sauran shuwagabanin jama’a da suke tabbatar da fadakarwa kan muhimmancin rigakafi domin samun nasarar da aka sanya a gaba a kowani lokaci.

Ita dai Makon rikafi ta Nahiyar Afirka wanda ake gudanarwa a dukkanin watan Afrilun kowace shekara domin wayar da kai da kuma fadakar da jama’a muhimmancin hakan.

Kayayyakin jinyar da NAWOJ suka raban dai dukkaninsu sun jibinci kula da lafiyar jarirai ne da kuma na mata masu juna biyu gami da na kula da tsaftar iyali, wanda aka kiyasce kudinsa na dubban nairori.

 

Exit mobile version