Kungiyar Matasan Arewacin Nijeriya (NYCN) ta yi Allah wadai da hare-haren da ke ta faruwa a yankin Kudu maso yammacin Nijeriya. Hakazalika ta bukaci gwamnatin tarayya da ta gaggauta daukar mataki kan lamarin.
Kungiyar ta nuna damuwarta kan yawan hare-haren da ake kaiwa kan ‘yan Arewa, musamman harin baya-bayan nan a kasuwar Sasha ta karamar Hukumar Akinyele da ke jihar Oyo.
Wata sanarwa daga kakakinta, Mock Kure, ta ce: “Hankalin Majalisar Matasan Arewacin Nijeriya ya karkata ne kan barna da ake yi wa ‘yan Arewa, musamman a Kasuwar Sasha ta Karamar Hukumar Akinyele, Jihar Oyo, Kudu maso Yammacin Nijeriya.
Kungiyar ta lura da boyayyar manufar da ake da ita na korar ‘yan Arewa mazauna yankin, tare da yin kira ga dukkan makiyaya da gwamnan Ondo Rotimi Akeredolu, da su bar Mazaunan Gandun Dajin jiharsa.