Kungiyar matasan Arewa (Coalition of Northern Youth Groups CNYG) ta janye wa’adin da ta ba ‘yan kabilar Igbo na su tattara Inasu-Inasu su koma yankinsu a duk jihohin arewa 19 kafin 1 ga watan Oktoba.
Kungiyar ta sanar da hakan ne a wani taron da ta yi a Otel din Transcorp dake Abuja.
Taron kngiyar ya samu halartar wasu daka cikin dattijan Arewa da kuma sarakunan Igbo, Gwamnan Jihar Borno na cikin wadanda suka samu damar halartar taron, kamar yadda kakakin kungiyar (CNYG), Alhaji Abdulaziz Sulaiman ya bayyanawa manema labarai.