Mahdi M Muhammad" />

Kungiyar Matasan Arewa Ta Nemi Afuwar ’Yan Biyafara

A ranar Juma’ar da ta gabata ne ’yan Kungiyar Matasan Arewa, Arewa Youth Consultatibe Forum (AYCF), su ka halarci taron ’yan kabilar Igbo masu rajin tabbatar da Biyafara a matsayin kasa daga Nijeriya, inda su ka nemi afuwarsu bisa wata sanarwa da AYCF din ta taba bayarwa shekaru uku da su ka gabata na bayar da umarni korar dukkan ’yan kabilar ta Ibo da ke zaune a Arewacin Nijeriya.

Shugaban Kungiyar na Kasa, Alhaji Shettima Yerima, ne ya nemi wannan afuwa a yayin da ya jagoranci wasu shuwagabannin matasa na Arewa a wata ziyarar da su ka kai wa Mista Ralph Uwazuruike, shugaban kungiyar gwagwarmayar kafa kasar Biyafara (MASSOB) da kungiyar rajin neman kafa sabuwar kasar, wato Biafran Independent Mobement (BIM), a Owerri ranar Juma’ar da ta gabata.

Yerima ya bayyana cewa, ya zo ne domin neman hadin kai a tsakanin ‘yan kabilar Igbo da ‘yan Arewa ta yadda kabilun biyu za su iya zama cikin jituwa a ko’ina a cikin kasar.

Yayin da ya ke karin haske game da sanarwar dakatarwar ta baya, Yerima ya ce, kungiyar ta yi nadama game da matsalolin da umarnin ya haifar wa kabilar Igbo da ke zaune a Arewa a lokacin.

Ya cigaba da cewa, “manufar dakatarwar ita ce, don fallasa gurbatattun shugabannin Igbo da kuma kada su haddasa rikici tsakanin kabilun biyu. Daga yanzu, AYCF za ta dauki nauyin kare ’yan kabilar da ke zaune a arewacin kasar. Wasu abubuwan su na aiki ne da hamayya da Igbo a Arewa, shi ya sa mu ka bada umarnin korar, amma yanzu mu na son tabbatar wa duniya cewa, har yanzu kabilun biyu su na tare.”

Ya kara da cewa, “na zo ne, don na yi jawabin zaman lafiya da hadin kai da samar da zaman lafiya tsakanin kabilar Igbo da ‘yan Arewa saboda muna son ganin cewa kowa a kasar ya zama daya. Mun yi nadamar matsayinmu na farko game da Igbo a arewa, muna kara neman kwanciyar hankali wanda zai kawo zaman lafiya tare da tabbacin tsaron Igbo a Arewa, domin zaman lafiya.”

Daga karshe ya bayyana cewa, zai tabbatar da cewa ba za a kara musgunawa ‘yan arewa ba ko tsoratar da su a jihar Imo ba, kuma ya yi gargadin cewa duk wani harin da aka kaiwa ‘yan Arewa a jihar Imo sun yafe.

Idan dai za a iya tunawa, Matasan Arewa sun bayar da sanarwar dakatar da umarnin ba wa Igbo da ke Arewa damar fita daga yankin tuntuni.

Exit mobile version