Abubakar Muhammad Taheer" />

Kungiyar Matasan Birnin Kudu Ta Bai Wa Injiniya Dau Aliyu Lambar Yabo

Kungiyar cigaban matasan Birnin Kudu ta bada lambar yabo ga wakilin mazabar Birnin Kudu da Buji a majalisar wakilai ta kasa Injiniya Magaji Dau Aliyu a garin Birnin Kudu.

A jawabinsa wajen bikin Gwamnan Matasa na Birnin Kudu Alhaji Bashir Mango ya yaba da nasarorin da dan majalissar ya samu a zangonsa na farko.

Yace Dau ALiyu ya bada gagarumar gudunmawa wajen cigaban mazabarsa a bangarorin samarda ruwansha da bunkasa tattalin arzikin matasa da samar da hanyoyin birji inda ya yi fatan hakan zai cigaba a zangonsa na biyu.

A jawabinsa dan majalisar wanda ya samu wakilcin mataimakinsa na musamman Barista Murtala Isa Abubakar ya yabawa kungiyar bisa wannan karamci tare da alkawarin ninkawa akan aiyukan dad an majalisar ya gudanar da zangon farko.

Hakazalika an bada takardun yabo ga gwamnonin matasa Gwaram da Dutse da Kiyawa da Jahun da Bamaina da Takur.

Tun farko Gwamnan matasan na Birnin Kudu ya bada gudunmawar sabulai da Omo da sauran kayayyaki ga babban asibitin birnin kudu da gidan yarin Birnin Kudu da gidan tsofaffi da kuma kai ziyara zuwa babban liman garin Birnin Kudu da kuma malamin alkurani alaramma Lawan Dan Jajire.

Exit mobile version