Kungiyar Mazauna Abuja Ta Yi Maraba Da Sakin El-Zakzaky

Kungiyar Mazauna Abuja mai suna a turance ‘Concerned Abuja Residents’ ta bayyana matukar jin dadinta da hukuncin kotun da ya saki Jagoran ‘Yan Uwa Musulmi da aka fi sani da ‘yan Shi’a; Sheikh Zakzaky da mai dakinsa Malama Zeenah. Abinda ya fi burge Kungiyar shine daina Zanga-Zangar Lumana da magoya bayan Malamin suka yi, wacce sun shafe shekara 4 suna yin ta ba kakkautawa.

Kungiyar ta kuma bayyana cewa ta samu wani rahoto da ke cewa Malamin da mai dakinsa sun taho Abuja tun da aka sake su, da zimmar su fita kasar waje don kula da lafiyarsu, amma rahoton da kungiyar ta samu na nuna cewa har yanzu hukumomi basu saki takardun tafiyar El-Zakzaky ba, a cewar kungiyar ta samu wannan bayanin ne daga majiya mai tushe.

Mai magana da yawon kungiyar Ayinde Danjuma Abdul, ya bukaci Shugaban Kasa Buhari da ya gaggauta bada umarnin sakin takardun mutanen, saboda a cewarshi ba sa bukatar a ce mabiyan Shehin Malamin sun dawo da zanga-zangar a kan titunan birnin Tarayya Abuja, duk da a cewarsu Zanga-Zangar Lumana ce, kuma ba ta da matsala a dokar kasa, amma bai kamata a sake komawa gidan jiya ba.

Exit mobile version