Idris Aliyu Daudawa" />

Kungiyar Miyyeti Allah Ta Nemi A Dakile Bazuwar Makamai A Nijeriya

Reshen kungiyar Fulani ta Miyetti Allah masu kiwon shanu ta Nijeriya rashen jihar Kebbi (MACBAN) ta yi kira da Hukumomin tsaro, a Nijeriya da cewar su kwace makaman da aka shigo da su ba tare da izini ba, da kuma wurin mutanen da basu da izini.
Shugaban kungiyar na jihar Kebbi Alhaji Muhammad Ardo-Zuru shi ne wanda ya bayyana haka loakcin da yake ganawa da manema labarai a Birni Kebbi.
Ya ci gaba da bayanin cewar “ Ci gaba da zaman cikin lafiya ba zai kasance sosai ba, muddin dai aka bar ire-iren wadannan muggan makamai suna hannu wasu mutane, wadanda suke masu aikata laifi ne.
“ Idan dai har ana son zaman lafiya ya dore a kasa akwai bukatar su Hukumomi, su dauki matakai masu tsanani, domin kwace makamai daga hannun masu aikata laifi.
Kamar yadda ya kara jaddadawa“Wannan ya kamata ya hada da hukunta wadanda aka samu da makaman da ake amfani dasu wajen kashe mutane wadanda basu ji, basu gani ba, koda kuwa mutum wanene shi sai an hukunta shi”.
Ardo-Zuru, ya bayyana sha’awar shi ta kungiyar Miyyeti Allah ta hada kai da gwamnati da kumka Hukumomin tsaro, saboda asamu dorewar zaman lafiya.
“Bamu bada goyon baya cewar al’umma su dauki doka a saboda kawai su kare kansu wannan ba magana bace.hannun su.
“Wadanda suke da hannu a kisan kan da ba’a dade da yi ba, wannan ya nuna ke nan kamar ma suna son su tunzura sauran sassan kasa, domin su samu damar wargaza kasa”.
”An kashe mana mambobi aduk fadin Nijeriya amma kuma a matsayin mu na Shugaban, ba zamu basu damar su dauki fansa ba.
“Saboda mun gano cewar wadanda suka kai ma Fulani hari a Jihohin Taraba, Binuwai, da kuma Kaduna, sun kai wadannan hare- haren ne, saboda kawai su wargaza kasa”.
Amma duk da haka Ardo-Zuru daga karshe ya bayyana cewar kungiya za ta hada kai da kunghiyar Lauyoyi ta kasa (NBA) Attoni janar kuma babban mai shari’a na kasa, da kuma kwamishinonin shari’a na jihohi masu yawa, da cewar a gaggauta sakin Fulani wadanda ake tsare dasu, wadanda kuma basu ji basu gani ba, da ake tsare dasu a gidajen Fursunoni daban- daban a Nijeriya.

Exit mobile version