Kungiyar Musulmin Jihar Kogi Ta Yi Bikin Sabuwar Shekarar Musulunci

Kungiyar al’ummar musulmi a jihar Kogi (KOSMO) karkashin laimar Jama’atul Nasrul Islam (JNI)a jiya alhamis ta gudanar da bikin shiga sabuwar shekara ta addinin Musulunci, wato 1 ga watan muharram 1442, wadda ta zo daidai da 20 ga watan Augusta,2020 miladiyya.
Bikin wanda ya samu halartar al’ummar musulmi daga sassa dabam dabam dabam na jihar, an gudanar da shi ne a katafaren dakin taro na masallacin Isah Kutepa dake garin Lokoja, babban birnin jihar ta Kogi.

Da yake gabatar da lakca mai taken” Cutar Korona” darasi da kuma kalubale ta fuskar addinin Musulunci, babban mai jawabi kuma alkali a kotun daukaka kara ta addinin Musulunci ta jihar Kogi, mai shari’a Ibrahim Ohu, kira ya yi ga al’ummar musulmi da su koma ga Allah( SWT) tare da neman gafara daga ubangiji wanda shi ne ke yaye ko wace irin bala’i komin girmanta.
Mai Shari’a Ohu ya kuma danganta bullar cutar ta korona bairos da  yawan laifufuka da suke afkuwa a doron kasa.
Cikin laifufukan da mai shari’a Ohu ya zayyano sun haxa da zinace-zinace da luwaxi da maxigo da cin amana da cin hakkin marayu da zub da jinin al’umma babu gaira babu dalili da dai sauran laifufuka makamantansu.
Malamin addinin Musuluncin daga nan ya yi kira ga Musulmi da su koyi darasi a sakamakon bullar cutar ta korona wanda ta addabi duniya baki daya.
Ya kuma yi kira ga Musulmi da su bi dokokin da hukumar yaki da cuttuka ta kasa(NCDC) ta gindaya da suka haxa da rufe fuska da amawali da wanke hannu da sabulu da kuma nisanta juna a yayin cuxanya.
Mai shari’a Ibrahim Ohu daga nan ya kalubalanci gwamnatoci a dukkan matakai da su inganta cibiyoyin kiwon lafiya domin dakile cututtuka daban-dabam da  samar da abubuwan inganta rayuwar al’umma da kuma bullo da shirye-shirye da kuma tsare tsaren da za su kyautata rayuwar al’umma.
Shugaban kungiyar Jama’atul Nasrul Islam(JNI) na jihar Kogi,Ambasada Usman Bello a nasa jawabin, ya bayyana shekarar a matsayin shekara mai muhinmanci a tarihin addinin Musulunci, ganin cewa shekara ce da Annabi Muhammadu (SAW) da ‘yan tsirarun musulmi a waccan lokacin suka yi hijira daga makka zuwa madina domin kauce wa zalunci da kuma azabar kafiran makka.
Ambasada Bello daga nan yayi kira ga Musulmi dasu yi amfani da bikin don koyar darasi domin ci gaba da cin gajiyar dauriya da hakuri da son juna da kuma kauna kamar yadda fiyayyen halitta,Annabi Muhammadu (SAW) ya yi a lokacin da yake raye.
Tunda farko a nasa jawabin, Kodinetan kungiyar musulmi ta jihar Kogi (KOSMO), Malam Nasiru Yusuf Abdallah Al,Lokoji, ya gode wa wadanda suka ba da gudunmwarsu wajen ganin an samu nasarar shirya taron na shiga sabuwar shekarar ta addinin Musulunci.
Muhimman abubuwan da aka gudanar a wajen bikin sun hada da kaddamar da kalandar addinin Musulunci na sabuwar shekarar da kuma karrama wasu mutane uku da suka bada gudunmawarsu wajen ciyar da addinin Musulunci gaba a jihar Kogi.
Mutanen sun hada da Alhaji Yusuf Abdullahi Ohikura da Dakta  Aliyu Idris da kuma Alhaji Abdulkareem Jami’u Asuku wanda shi ne babban hadimin gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi.

Exit mobile version