Kungiyar NAFOWA Ta Kaddamar Da Makaranta Don Inganta Ilimin Yara A Bauchi

NAFOWA

Daga Mahdi M. Muhammad, Abuja

Kungiyar matan manyan jami’an sojojin saman Nijeriya (NAFOWA) a ranar Litinin, 21 ga Disambar, 2020, ne ta kaddamar da wata makaranta mai suna ‘NAFOWA Little Angels’ da ke sansanin sojin saman Nijeriya (NAF) a Bauchi, don amfanin ’ya’yan sojoji da kuma sauran al’umma.

Daraktan hulda da jama’a da yada labarai na rundunar sojin saman, Air Vice Marshal Ibikunle Daramola, ne bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu, inda ya nakalto Shugabar kungiyar NAFOWA ta kasa, wacce kuma ta kasance babbar bakuwa a wurin bikin, Hajiya Hafsat Sadikue Abubakar, tana bayyana cewa, yanke shawarar gina makarantar ‘NAFOWA Little Angels’ da ke Bauchi ya samo asali ne daga sha’awar bayar da gudumawa don samar da ingantaccen ilimin farko na yara da kuma sassan ma’aikata a sansanin NAF da ke Bauchi, da kuma sauran al’ummomin da suka karbi bakuncin.

Ta kara da cewa, makarantar ‘NAFOWA Little Angels’ Bauchi zata tallafawa kokarin NAF wajen biyan bukatun walwalar ma’aikata a bangaren bukatun ilimin yara.

Da ta ke karin bayani, Hajiya Hafsat ta bayyana cewa, NAFOWA ta maida hankali ne kan samar da ingantaccen ilimi a cikin aminci da tsaro.

“Kungiyar ta kuma mai da hankali kan samar da wurin Kula wa da yara, wasanni, makarantun Nasiri da Ilimin musamman na zamani, da nufin gina tushen ilimi mai karfi gaske a farkon rayuwar yara”, in ji ta.

Shugabar NAFOWA na kasa, wacce ta yi matukar farin ciki kuma ginin ya burgeta, ta yaba wa Shugabar NAFOWA, Kwamandan ayyuka na musamman (SOC), Misis Jummai Ohwo, game da kyakkyawan aikin wanda ya kasance abin yabo, wanda kuma aka kammala shi cikin kankanin lokaci, duk da kalubalen da ake fuskanta ta annobar korona.

Hajiya Hafsat ta umarci manyan malamai da ma’aikatan Makarantar da su yaba da irin sadaukarwar da aka yi don samarwa makarantar kula ta yadda ya dace. Ta kuma yaba wa shugaban hafsan sojojin sama (CAS), Air Marshal Sadikue Abubakar, saboda nuna goyon baya da karfafa gwiwa ga NAFOWA, yayin da ta yaba da gudummawa da goyon bayan Kwamandan Sojin sama (AOC) SOC, Air Vice Marshal Charles Ohwo, kazalika da sauran hafsoshin SOC.

Tun da farko a jawabinta na maraba, Shugabar na ‘NAFOWA SOC Chapter’, Jummai Ohwo, ta bayyana cewa, kafin yanzu sansanin NAF Bauchi na da duk abubuwan da ake bukata na zamantakewar jama’a, amma ba su da makarantar kulawa ko na renon yara. Iyalan ma’aikata sai sun yi tafiyar kimanin kilomita 35 don samun damar wannan muhimmin matakin na koyon karatu. Ilimi shine ginshkin rayuwa kuma mafi karfin abu wanda zai iya sanya mafi yawan burinmu ya zama gaskiya, saboda haka larura ce da kuma saka jari wanda dole ne a runguma tare da muhimmancin da ya kamata.

Misis Ohwo ta kara da cewa, makarantar ‘NAFOWA Little Angels’ Bauchi, a matsayin wani yanki mai dauke da fasali irin na L da ke dauke da ofishin Babban Malamin, da Ofishin Ma’aikata, da ajujuwa 5, da wurin kula da marasa lafiya, da dakin sauyawa, dakinda na’urar komputa da kuma bayan gida, da kayan aikin koyo na zamani.

Misis Ohwo ta kuma godewa Shugabar NAFOWA na kasa kan kyakkyawan shugabancinta da kishin ta na taimakon marasa karfi.

Bikin ya samu halartar mambobin kwamitin NAFOWA na kasa, Shugabannin kwamandoji da shuwagabannin sashin na Bauchi na sojojin Nijeriya da kungiyoyin mata na ‘Paramilitary Officers’ da kuma manyan shuwagabannin SOC da kuma kwamandojin hadin gwiwar ‘NAF Units’ a Bauchi, da sauransu.

Exit mobile version