Kungiyar ma’aikatan jami’o’i, NASU, reshen jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya ta bi sahun takwarorinta na.sauran jami’o’i wajen gudanar da zanga-zangar gargadi ga gwamnatin tarayya.
Da sanyin safiyar ranar Laraba, 13 ga Janairu, 2021, mambobin kungiyar suka yi dandazo a harabar jami’ar tare da rera wakokin neman ‘yanci.
Wakilin LEADERSHIP A YAU na daya daga cikin wakilan kafafen yada labarai da suka shaida yadda al’amarin ya gudana.
Kungiyar ta bayyana wasu koke-koke da korafe-korafe da gwamnati ya kamata ta sauraresu amma abin ya ci tura, bisa haka ne wakilinmu ya nemi jin ta bakin sakataren kungiyar Kwamred Emmanuel Adugwu dangane lamari don haka ne take ya bayyanawa duniya bukatun nasu, kai tsaye kuma ya fara ne da cewa, “dalilin yin wannan zanga-zangar tamu shine muna neman hakkokinmu ne daga gwamnatin tarayya, tun Oktoba akwai maganar alawus dinmu, akwai ariyas na mafi karancin albashi, akwai rashin bin tsari wajen biya da IPPS, akwai kin yin yarjejeniya tsakanin kungiyar mu wanda gwamnatin tarayya ta yi da kuma rashin biyan mambobinmu da suka bar aiki. Shi ya sa muka fito domin nunawa gwamnatin tarayya cewa ba ta dube mu ba, ba ta yi gyara ga al’amurran da muka bayyana ba.”
An yi taro lafiya an tashi lafiya.