Kungiyar Ndigbo Ta Ce  Ba Za Ta Yi Watsi Da Nnamdi Kanu Ba  

Kanu

Daga Idris Aliyu Daudawa,

Yayin da ake ci gaba da sauraren karar jagoran kungiyar mai fafutukar samun  kasar Biyafara (IPOB), Nnamdi Kanu jiya, wata kungiyar ‘yan kabilar Ibo mai suna Ndigbo United Forum (NUF), ta bayyana cewa ba zata taba sa ido tana ganin ta bar Nnamdi Kanu yana kasancewa cikin wani hali ba.

Kungiyar wadda ta bayyana Kanu a matsayin mutum wanda yake babban “jarumine dan kabilar Ibo,”inda kuma ta ce kungiyar za ta ci gaba da tsayawa tare da shi ba tare dayin la’akari da kalubalen da yake gaban sa ba, inda ta kara jaddada cewa halin da gwamnatin Nijeriya ta sa su al’ummar Igbo, hakan ne ya haifar da irin halin da ake ciki wajen fafutukar tasu .

Wata sanarwar da ta fito bakin shugaban kungiyar amintattu ta kungiyar,, Cif Chinedu Mba, ya bayyana cewa ya kamata kowa da kowa, musamman ma su ‘yan kabilar Igbo yadda suka tashi tsaye suna nuna rashin goyon bayan rashin adalcin da ba ayi masa ba.

Ya ci gaba da bayanin cewa: “A bayyane ne shi al’amarin yake karara irin rashin adalcin da ake yiwa ‘yan kabilar Ibo, ya ce abin yafi munana ne a kar kashin mulkin shugaban kasa Muhammadu Buharl. Kamar dai yadda ya ci gaba dakarin bayani abin ya nuna yadda wasu al’amura suke tafiya kamar  ma ana yin abin ne domin a musgunawa su ‘yan kabailar Igbo,wannan kum ba tare da ana yin la’akari da irin gudunmawar da suke badawa ba, ta ci gaban tattalin arziki.

 

Ya kara jaddada cewa ” Kasar Nijeriya tana da manyan harsuna uku wadanda suke ana ji da su, da suka hada da – Igbo, Hausa da Yarabawa. Daga cikin su kabilun uku,cikin ‘yan kabilar , Ndigbo ne kawai suka fi nuna damuwar su da kuma nuna son ita Nijeriya, saboda kuwa ko ina mutum yaa je zai same su a Nijeriya ko wanne sko da kuma lungu. Duk kuma wanda yake maganarcewar su ‘yan kabailar na Igbo basu son Nijeriya, wannan magana cedai wasu suke yi kawai. ‘Yan kabilar na IUbo sune suka fi kowa son Nijeriya ta ci gaba da tafiya a matsayin ta na kasa daya  kuma al’umma daya.

 

Ya ci gaba da bayanin cewa domin  nuna cewa suna matukara  son Nijeriya, shi ma yasa suka amince suke zama sassa daban daban na Nijeriya domin du bunkasa tattalin arzikin ita Nijeriya.

 

Mba ya yi kira da masoya adalci da su tashi tsaye wajen nuna rashin yadda dakin yin shi adalci lokacin da ya dace ayi shi, su kuma suna tare da shi Kanu a wannan lokacin daya fi dacewa ace ana nuna ana son shi, wato lokacin daya fi son yaga ana nuna ana tare da shi. Ya kuma ce cigaba da ake yi na tsare shi wani abu ne wanda ya shafi al’amarin cin mutuncin dan Adam, idan kuma aka ci mutucin mutum daya tamakar maa n ci mutuncin mutane da yawa ne. Hakanan kuma shi al’amarin daya shafi  tauye ma wani ‘yancin kansa, duk kuma wani cin mutuncin da aka yi ma wani, cin mutunci ne ga wasu. Dukkan kungiyoyi mutane daban- daban ya dace su su tashi tsaye su nuna rashin mu’amala da rashin adalci.

 

Shi ma lauyan Kanu, Aloy Ejimakor, a jiya ne ya yiu kira da jami’an tsaro kada su tada hankalin su magoya bayan Kanu domin za su zo Abuja ne daga wurare daban- daban , domin su nuna goyon bayan su gare shi, ko kuma  akama su.

 

 

Ejimakor ya yi wannan kiran ne a wani bayanin daya aikewa jaridar The Guardian inda yake nuna cewa shi bayanin akwai dalilin da suka sa aka yi su, domin ya ce mutanen daza su zo Abuja domin su nuna goyon bayansu ga Mazi Nnamdi Kanu, wata kila kodai jami’an tsaro za su iya tayar masu da hankali ko kuma kama su.”

Amma duk da hakan ya ce shi bai cewai ko wasu su zo Abuja ba domin ci gaba da sauraremn shari’ar da za ayi ranar Litinin 26 ga watan Yuli na wannan shekara, ya kuma duk wanda yake ganin za i zo to fa yana iya zuwa amma kuma baba bukatar wani al’amrin daya shafi tada hankali a wurin.

Ya kuma ce daga karshe ita shari’ar da ake yi ta Kanu ba aboye bane za ayi ta, a kuma tuna da cewa shi mutum ba a iya cewa mai laifi bane, har sai an kammala bincike tukunna ba a same shi da aikata laifi ba.

Exit mobile version