Kungiyar kolin tattalin arziki a Nijeriya (NESG) ta shawarci gwamnatin tarayya da ta dunga daukan matakin da suka dace wajen tattalin arziki, domin samun nasarar farfado da ayyukan tattalin arziki a shekarar 2021.
Kungiyar ta bayyana cewa, matakin da gwamnatin tarayya ta dauka na rufe iyakokin kasar nan ko kadan ba su dace ba, babu wani abin da ya haddasa sai dai karin matsalolin tattalin arziki a cikin kasar.
Kungiyar NESG ta bukaci gwamnatin tarayya a kan ta dunga tantubar masu ruwa da tsaki kafin ta yanke duk wani hukunci akan tattalin arziki.
“Rufe iyakokin kasar nan mataki ne wanda ko kadan ba su dace ba. Ko kafin ballowar cutar Korona, kaddamar da matakin rufe iyakokin kasar nan tafkar toshe samun kudaden haraji na shigowa da kayayyaki a cikin kasar.
“Sakamakon haka ne farashin kayayyaki suna yi tashin gwauron zabi a cikin kasar nan tun daga kashi 11 na watan Agustan shekarar 2019 har zuwa na kashi 14.9 na watan Nuwambar shekarar 2020. An samu koma bayan tattalin arziki wanda ba a taba samu ba tun kafin shekarar 2019.
“Rufe iyakokin kasar nan mataki ne da ke kuntata wa kamfanoni masu zaman kansu musamman ma wadanda suke cikin kasuwancin saye da siyarwa na cikin gida da kuma na kasashen ketare,” inji kungiyar.
Kungiyar ta bukaci gwamnatin tarayya da ta daina daukan matakai masu tsauri wadanda za su raunata tattalin arzikin kasar nan tare da daukan matakin farfado da harkokin kasuwanci a nan cikin gida da kuma na kasashen ketare.
“Nijeriya ta kaddamar da wasu matakai na kawo sauyi a shekarar 2020, wanda ya hada da cire tallafin man fetur da na wutar lantarki wanda wnnan babban barazana ce ga mutanen kasar nan.
“Ya kamata idan gwamnatin tarayya za ta dauki wannan mataki da dunga la’akari da harkokin kasuwanci wanda zai safi zuwba jari da kuma wasu ayyukan tattalin arziki.
“Ya kamata gwamnatocinjihohi su dunga bai wa majalisa bayanan na matakan da ya kamata a dauka a kan tattalin arziki a yankunansu, ta yadda za a samu ra’ayin mutane wanda zai dace da duk wani mataki da za a iya dauka a bangaren tattalin arzki. Ya kamata gwamnatin tarayya ta dauki matakan gyara a bangarorin tattalin arziki tare da yin la’akari da wasu illoli a kan duk matakin da za ta dauka na tattalin arziki.