Abdullahi Sheme" />

Kungiyar Noman Auduga Ta Raba Irin Auduga Da Taki A Katsina

Kungiyar noman auduga ta kasa reshen jihar Katsina ta raba irin auduga da maganin kwari hade da takin zamani na daminar bana ga ’ya’yan kungiya 10,357 afadin jihar Katsina a karshen watan Satumba na wannan shekarar da mu ke ciki.

Wannan tabbaci ya fito ne daga bakin sakataren kungiyar na jiha, Alhaji Abdulsalam Musa Kafur.

A lokacin da wakilanmu su ka ziyarci inda a ka raba kayan ga nambobin kungiyar a Jabiri Funtua, ya iske mutanen kananan  hukomomin Faskari, Danja Funtua da karamar hukumar Bakori, su na karbar irin auduga buhu daya da buhun taki shida da maganin feshi lita takwas da fanfon feshi guda daya ga kowanne manomin auduga, wanda zai noma hekta daya ta auduga a gonarshi.

Kungiyar noman auduga ta kasa reshen jihar sun raba kayan noman auduga a shiyoyi shida a fadin jihar shiyoyin sune Ingawa, Dandume, Kafur, Katsina, Funtua da shiyar Malumfashi sama da manoma 10,357 suka amfana da shirin bashin noman auduga a fadin jihar Katsina.

A binciken da wakilan mu ya gudanar yagano wasu manoma da yawan gaske anan take suke siyar da kayan da aka basu wakilanmu yazanta da wasu daga cikin wadanda suka amfana da shirin bashin noman audugar wadanda suka bukaci a sakaya sunayensu da kananan hukumominsu, sunkoka kwarai sunce yakamata abasu kayan tun cikin watan shida wato watan june  na kowacce shekara amma ba’a bada ba sai cikin watan tara wato satumba kenan anyi latti, shiyasa suke saida kowanne buhun takin kamfa dan buhari akan naira dubu uku kuma sun karbi bashin kowanne buhun taki akan kudi naira dubu bakwai sannan kowanne litar maganin feshi suna saidashi akan naira dari tara tara, lita takwas akan naira dubu bakwai da dari hudu N7,200 maimakon naira dubu daya dari hudu lita takwas dubu shadaya da dari hudu a yadda aka basu bashin.

Wakilanmu ya zanta da shugaban shirin na shiyar funtuwa Alhaji Hamisu malumfashi. Yace manoman zasu biya bashin a tsakanin watan farko zuwa watan ukku na sabuwar shekara mai zuwa, sakateran kungiyar na jihar katsina Alhaji Abdulsalamu Musa kafur kuma shine ko,odineta na kasa a jihohi sha daya jihohin sune Kaduna, kwara, Gombe, Adamawa, Neja, Katsina, Zamfara da sauran jihohin da ake noman auduga.

Alhaji Abdulsalam yaci gaba da cewar sama da manoman auduga dubu talatin da biyar N35, 000 suka amfana da shirin bashin noman audugar na daminar bana.

Alhaji Bature Tafoki ya yaba da shirin bashin noman audugar domin a bunkasa noma saboda tun zamanin turawa ansan yankin, Funtuwa  da malumfashi wajen noman auduga yace a jahohin arewa babu inda ake noma  auduga irin yankin Funtua a jihar Katsina da jihar Gombe zuwa Adamawa, ya ce, yakamata manoma su gode wa shugaban kasa Muhammadu Buhari wajen inganta kasa da abinci da kuma yaba wa shuwagabannin kungiyar noman auduga ta kasa musamman shuwagabannin kungiyar na jihar Katsina domin sunyi kokari sosai wajen taimakon membobin kungiyar ya ce babu shakka noman auduga ya inganta kuma ya karu da kashi hamsin cikin dari.

Exit mobile version