Daga Balarabe Abdullahi, Zariya
A ranar Asabar da ta gabata,kungiyar direbobin manyan motoci a karkashin kungiyar NURTW reshen karamar hukumar Zariya a jihar Kaduna,ta kaddamar da sabbin shugabannin kungiyar reshen Galma,da aka zabe su a kwanakin baya.
Alhaji Kabiru Tanko, shi ne shugaban kungiyar reshen karamar hukumar Zariya, a jawabinsa a lokacin kaddamar da sabbin shugabannin, ya bukaci sabbin shugabannin da lallai ne duk abin da za su yi su bi dokokin kungiya, ya ce in wani abu kuma ya shige musu duhu,ya na shirye a kowanne lokaci ,ya ba su shawarar da za su aiwatar da ayyukansu, kamar yadda kundin tsarin mulkin kungiyar ta tsara.
A dai jawabinsa, Alhaji Kabiru ya tunatar da su cewar, sai fa sun hada kansu ne a matsayinsu na shugabanni za su sami nasarar duk wani aiki ko kuma ayyukan da suka sa a gaba da ya shafi kungiya ko kuma ciyar da membobin kungiya gaba a kowane fanni na rayuwa.
Da kuma shugaban ya juya ga membobin kungiyar, ya shawarce su da su ba wadanda suka zaba duk hadin kan da suka dace,domin su sami damar gudanar da ayyukan da aka dora ma su, da suka shafi ’ya ’yan kungiyar ko kuma wadanda kungiyar za ta yi mu’amala da su, wato direbobin manyan motoci da suke daukar kaya.
A karshen jawabinsa, Alhaji Kabiru Tanko,ya nuna matukar jin dadinsa da kuma gamsuwa na yadda mambobin kungiyar suka yi zabe ba tare da tayar da jijiyar wuya ba.Ya ce ya na fatan shugabannin kungiyar za su jagoranci kungiyar nan da shekara hudu da tsarin mulkin kungiyar ya tanadar ma su.
Shi ko sabon shugaban Alhaji Haruna Nuhu,da farko nuna godiyarsa ya yi ga Allah madaukakin sarki,da ya dora ma sa wannan nauyi na shugabancin wannan kungiya, ya ce ya na yin kira ga sauran wadanda aka zaba a mukamai daban-daban da su ba shi goyon baya, domin ya sami saukin jan ragamar kungiyar, kamar yadda dokar kungiyar ta tsara.
Da kuma ya juya ga direbobin manyan motoci da kungiyar za ta yi hulda da su, ya ce da yaddar mai duka za su shinfida adalci ga duk wani direba da ya je wannan reshe da ke Galma, sai kuma ya ce ya na fatan suma direbobin za su bi dokokin da a kungiyar ta tsara.
Sauran wadanda aka zaba sun hada da Haruna Bawa,mataimakin shugaba, sai Ya’u Musa sakatare sai Shehu Yahuza, mataimakin sakatare, sai Muntari Umar, ma’aji, sai Bashir Shehu, sakataren kudi, sai kuma Abdulhamid Magaji aka zade shi a matsayin sakataren shirye-shirye na wannan kungiya.
Sauran wadanda aka zaba sun hada da Ibrahim Hudu, mai bincike sai Kabiru Salisu,amintaccen kungiyar na daya sai Dauda Salisu amintaccen kungiyar na biyu, sai Hashimu Mohammed, jami’in ladabtar da masu laifi sai Alhaji Magaji, alkalin kungiyar, sai kuma Yusuf Tamamu, jami’in sintiri.