Daga Adamu Yusuf Indabo, Kano
Kungiyar mMarubuta ta ‘Potiskum Writers Association’ ta zama zakara ne a tsakanin kungiyoyin marubuta guda 32, wadanda suka shiga gasar muhawarar da aka yi a farfajiyar dandalin sada zumunta ta Bakandamiya, kuma manhajar ta bakandamiyar ce ta shirya, ta kuma dauki nauyinta.
Gasar mai taken ‘Bakandamiya 2020’, ita ce gasa ta biyu da manhajar ta Bakandamiyar ta sanya a tsakanin marubuta, domin kuwa a shekarar 2019 ma ta sanya gasar gajeren labari a tsakanin daidaikun marubuta, wacce Marubuci Kamal Muhammad Lawan (Kamala Minna) ya zama zakaran gasar.
Gasar muhawarar dai an yi ta ne a yanar gizo a cikin farfajiyar ta Bakandamiya, wacce aka fara ta a watan Didambar 2020 kuma aka gama ta a watan Janairun 2021, sannan aka yi bikin karramawa da bayar da kyaututtuka ga kungiyoyin da suka samu nasara a ranar Lahadin da ta gabata 07 ga Maris, 2021, a Birnin Kano.
Kungiyar Potiskum Writers da ta zo na daya ta samu awalajar kudi na wuri na gugar wuri har Naira 50,000 da tarin littattafai, domin yin nazari da kuma kambun girmamawa. ‘Hakuri Da Juriya Writers Association’ ita ce kungiyar da ta zama ta biyu a gasar, inda ta sami awalajar Naira 30,000 da kuma tarin littattafan nazari. ‘Hazaka Writers Association’ ce ta yi nasara a mataki na Uku. Ta samu awalar kudi Naira 20,000 da kuma littattafan nazari.
Sai kuma ‘First Class Writers Association’ da ta zo na hudu a gasar muhawarar, wacce ita ma ta samu kyautar kudi Naira 10,000 da kuma littattafan nazari. Haka sauran kungiyoyi 28 da suka shiga muhawaran sun samu takardar shaidar shiga gasar.
Taron bikin karramawar dai ya samu tagomashin halartar manyan baki da ‘yan jaridu da mawaka da suka nishadantar da taron da kuma marubutan da da na yanzu.
Manyan bakin sun hada da Alhaji Aminu Ala, wanda shine Babban Bako na Musamman, Farfesa Yusuf Adamu, Babban Bako Mai Jawabi, Alhaji Ado Ahmad Gidan Dabino (MON) a matsayin shugaban taro.
Sannan kuma akwai manyan marubuta irin su Sir. Bala Anas Babinlata, Aminu Abdu Na’inna, Dan’azumi Baba, Hafsat Abdulwahid, Balaraba Ramat da dai sauransu.