Kungiyar PTA Ga ‘Yan Bindiga: Ku Dubi Allah Da Alfarmar Ramadan Ku kyale Sauran Daliban Jami’ar Greenfield  

Daga Abubakar Abba,

kungiyar iyayen daliban makarantar Firmare ta kasa PTA, ta yi roko da tattausar murya ga ‘yan bindigar da suka sace, daliban jami’ar Greenfield da ke a jihar Kaduna da su dubi girman ubangiji ka da su kashe sauran daliban da ke a hannun su.

Ta kuma yi kira ga masu garkuwar d da su kara wa’adin da suka yanke na kashe daliban domin a samu a biya su kudin fansar daliban da suke ci gaba da rikewa.

Ta yi wannan kiran ne biyo bayan wa’adin da ‘yan bidigar suka bayar na awa ashirin da hudu na idan ba a biya kudin fansar sauran daliban ba, za su kashe su.

In ba a manta ba, ‘yan bindigar sun dage kai da fata cewa, sai an ba su naira miliyan 100 tare da kuma baburan hawa goma a matsayin fansa kafin su sako sauran daliban jami’ar Greenfield da ke a hannun su.

Kusan yau dai sati uku ke nan, daliban jami’ar ta Greenfield ke a hannun ‘yan bindigar.

A hirarsa da LEADERSHIP A YAU a kaduna, shugaban kungiyar ta kasa Alhaji Haruna danjuma ya bayyana cewa, ya zama waji a roki ‘yan bindigar domin suyi dubi kan lamarin domin a saukaka wa daliban da suke rike da su.

Alhaji Haruna ya ci gaba da cewa, akwai babbar matukar damu wa da tsoro a zukatan iyaye da daliban da suke rike da su tun bayan da masu garkuwar suka shelanta wa duniya cewa, za su hallaka sauran daliban da suke rike da su.

A cewarsa, rokon na su don sako sauran daliban jami’ar ya zama wajibi domin a samu daliban su dawo cikin koshin lafiya, inda ya kara da cewa, mun kadu matuka da jin matakin da jin furucin ‘yan bindigar suke son su dauka kan sauran daliban da suka rage a hannun su.

Ya bayyana cewa, abin takaici ne yadda ‘yan bindiga suka fito da sabon salon na karbar kudin fansa tsugugu daga gun iyaye ko kuma gwamnati.

Ya ce, ya zama wajibi gwamnati ta samar da matakan samar da kariya ga daukacin makarantun da ke a fadin kasar nan, musamman domin kare rayukan daliban.

Ya bayyana cewa, domin daragar da ke a cikin wannan watan na Ramadan, Ina rokon masu garkuwar ka da su kashe sauran daliban jami’ar Greenfield kamar yadda suka yi barzanar yi, inda kuma ya yi kira ga daukacin mabiya manyan addinai biyu Musulunci da kuma na Kirista da su kara zage wa wajen yin addu’oin domin Allah ya kawo karshen rashin tsaro da ya addabi kasar nan.

Exit mobile version