Connect with us

RAHOTANNI

Kungiyar RATTAWU Ta Jihar Kebbi Ta Yi Sabbin Shugabanni

Published

on

A ranar Laraba, Kungiyar RATTAWU ta kasa reshin jihar kebbi, ta gudanar da zaben Shugabanni a matakin jihar inda Umar Abubakar Kalgo ya zama sabon zababen shugaban kungiyar karo na biyu a jihar ta Kebbi.

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin shugaban kwamitin gudanar da zabe a jihar, kwamared Babangida Umar Zurmi yayin da yake bayyana sakamakon zaben.

Sauran wadanda aka zaba tare da shi a matsayin mukarrabansa don gudanar da shugabanci, wanda uwar kungiya ta kasa ta turo Jihar Kebbi domin gudanar da zaben sababbin Shugabannin a matakin jihar, sun hada da, Mataimakin shugaban kungiyar na kasa mai kula da jahohin Arewa maso Yamma, Abubakar Chika, da kuma Mataimakin Sakatare janar na kasa Benjamin Gudadu, domin tabbatar an gudanar da zaben shugabannin kungiyar, bisa karewar wa’adin mulki na su na shekara uku kacel.

An gudanar da zaben ne a dakin taro na kungiyar Malaman makarantun firamare wato NUT, dake a cikin GRA a Birnin-kebbi.

Shugabannin da aka zaba sun hada da Umar Abubakar Kalgo a matsayin shugaban kungiya, Faruku Shatima a matsayin Mataimakin shugaba, Taminu Lawal a matsayin Sakataren kungiya, Garba Muhammad Kola a matsayin ma’ajin kungiya da kuma Ladi Anthony a matsayar Sakatariyar kudi.

Sauran sun hada da Faruku Riskuwa Kalgo, a matsayin jami’an yada Labarai, sai Umar Muhammad Argungu a matsayin Mataimakin Sakataren kungiya da kuma Aminu Sani Argungu a matsayin mai-binciken kudi.

Yayin da yake gabatar da jawabinsa bayan bayyana sakamakon zabe, sabon zababen shugaban kungiyar, Umar Abubakar Kalgo ya fara da yi wa Allah godiya kan wannan ranar da ya nuna masa da jama’a suka kuma zabensa karo na biyu a matsayin shugaba.

Ya ci gaba da mika godiyarsa ga ‘yan kwamitin gudanar da zaben a karkashin jagorancin kwamare Babangida Umar Zurmi da kuma kulawar sauran manyan Shuwagabannin kungiyar na kasa da suka dafa masa baya wurin ganin an gudanar zaben cikin kwanciyar hankali ba tare da wata matsala ba. “Muna kara wa Allah godiya da dukkan Mambobin kungiya kan irin namijin kokarin da suka yi wurin tabbatar ganin na koma karo na biyu a matsayin shugaban, in ji Umar Kalgo.

” Da yardar Allah zan tabbatar da gaskiya da aldaci ga dukkan mambobin kungiyar ba tare da nuna wani banbanci ba” . Ya kuma roki dukkan mambobin da su hada kai domin a yi wa kungiyar aiki kamar yadda aka gudanar da mulki na farko. Ina godiya bisa da wannan karamci da aka yi min,”

Daga karshe ya yi kira ga mambobin kungiyar su sani cewa kofar ofishinsa a bude take don ba da shawara ko wata gudunmawa domin ci gaban kungiya da kuma mambobinta.

 
Advertisement

labarai