Daga Bello Hamza,
Shugaban kungiyar RTEAN na kasa, Alhaji Musa Muhammed Maitakobi ya nemi mambobin kungiyar su tabbatar da suna mutunta dokokin kasa a yayin da suke gudanar da ayyukansu a fadin kasar nan.
Alhaji Musa Muhammed Maitakobi ya bayyana haka ne a takardar sanarwa da aka raba wa manema labarai bayan bikin rantsar da sabbin shugabannin kungiyar na jihohin Gombe, Edo da kuma Anambra a hedikwatar RTEAN da ke Abuja inda aka samu halartar manyan lauyoyi da ‘yan jarida.
Ya kuma bukaci ‘yan kungiyar RTEAN da so sa ido a duk inda suke a fadin kasar nan su kuma hada kai tare da aiki tukuru da kuma kokarin wanzar da zaman lafiya a Nijeiya gaba daya.
Ya kuma shawwarci sabbin shugabanin kungiyar da su guji allubazaranci da kudaden kungiya su kuma guji gudanar da ayyukan da suka ci karo da tsrain mukin kungiyar, don kuwa kwamitin zartasarwa na kungiyar ta kasa na da hurumin rusa duk shugabanin da aka same da laifin karya dokokin kungiya.
Daga nan ya kuma shawarce su dasu mutunta dokokin tuki da na hanyoyi don ta haka ne za a tabbatar da rage yawan hatsarin da ake samu a kan hanyoyin kasar nan.
Ya ce, “A lokuttan baya mun gwada gudanar da zabe ta hanyar jefa kuri’a amma hakan ya aukar da rikici akan haka ne muka amince da zabar mutane don a tafi tare da kowa da kowa ba tare da samar da rikici ba”
Hakan kuma ya yi daidai da sashi na 6, 8(2) na tsarin mulkin kungiyar.
Daga nan ya bukaci gwamnati ta sanya ido akan irin tayoyin mota da ake shigowa da shi cikin kasa don suna daga cikin abubuwan da suke haifar da hatsurra a kasar nan, ya kuma bukaci mambobin kungiyar su hada hannu da jami’an tsaro a duk lokacin da bukatar haka ta taso.