Daga Idris Aliyu Daudawa,
Muhammadu Bello Dangaladima shi ne Sakataren tsare-tsare na kungiyar Sakkwata mazauna Abuja, a hirar da ya yi da LEADERSHIP HAUSA ya bayyana yadda kungiyar take taimakawa mambobinta.
Ya bayyana cewar kungiyar tasu tana da mambobi 5000 wadda take da shugaba daya da yake jagorancin kasar baki daya da sauran kananan shugabannin yanki wadanda suke kulawa da wuraren da ke karkashin babbar kungiyar.
Ya yi bayani inda ya ce da farko ana amsar Naira 100 daga ko wanne dan kungiya duk mako, daga baya kuma aka ga kudin sun yi kadan, aka dauki matakin kwanne shugaban yanki ya kawo Naira 1000. Ya ce wadannan kudaden da ake tarawa na mako, wani lokaci ana samun dubu hamsin, yayin da wani lokaci kuma fiye da haka.
Ya ci gaba ce idan wani al’amarin gaggawa ya taso, kowanne mamba yana ba da Naira dubu daya da za a hada gaba daya don a ga cewar an yi maganin matsalar.
Daga karshe ya ya ba da misali idan wani mamba ya shiga matsala sanadiyar halin rayuwa wato ya kasance babu kudaden da zai yi harkokin kasuwancinsa, akwai taimakon da ake ba shi domin ya ci gaba da gudanar da harkokin kasuwancisa. Ya kara da cewa shi yake yanke shawara kan ko nawa zai iya bayarwa a kowanne makon wajen biyan bashin da kungiyar ta taimaka masa.